Gwamnan Zamfara ya yi garambawul ga kwamishinoninsa

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi kwaskwarima tawagar kwamishinoninsa inda ya rantsar da sabon kwamishina.

A ranar Litinin ne gwamnan ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwar wanda a lokacin ne aka gabatar da rantsarwar.

A wata sanarwa da Kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, gwamnan ya yi ƙaramin gyara ne ga kwamishinonin nasa.

Bayan murabus da Mannir Mu’azu Haidara ya yi sakamakon lashe zaɓen ciyaman na ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda, sai aka naɗa Ƙasimu Sani Ƙaura a matsayin sabon kwamishinan don ya wakilci ƙaramar hukumar saboda jajircewarsa.

Gwamna Dauda ya ce hakan wani ɓangare ne na ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wajen tabbatar ajandar ceto al’ummar jihar.

Ya yi kira ga sabon kwamishinan da ya tabbatar da jajircewa wajen gudanar da ayyukansa.

Ya kuma taya shi murna tare da fatan ya yi aikinsa bisa gaskiya da adalci da kuma yi masa addu’ar samun taimakon Allah acikin hakan.

Sabon kwamishinan zai yi aiki ne a matsayin kwamishinan kula da Muhalli da Albarkatu ƙasa inda zai gaji Hon. Mahmud Mohammed Abdullahi, wanda aka mayar da shi Ma’aikatar Labarai da Al’adu.

Haka ma Hon. Nasiru Ibrahim Zurmi ya zama kwamishinan Gine-gine da Ci-gaban Birane inda ya maye gurbin Hon. Kabiru Koyi da aka mayar Ma’aikatar Kula da Ayyuka da Ƙaddamarwa.

Bugu da ƙari, Dakta Nafisa Muhammad ta koma Ma’aikatar Lafiya inda ta gaji Dakta A’isha M. Za Anka, wadda yanzu kuma ita ce kwamishinar Harkokin Mata da Ci-gaban Al’umma.

Zuwa nan da mako guda za kammala sauye-sauyen wuraren ayyuka tsakanin ma’aikatan.