Gwamnan Zamfara ya yi shiru kan rahoton damfarar sa jirgin Dala miliyan 6.3

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

A jiya Litinin ne, wata jarida mai suna ‘People’s Gazette’ ta ruwaito cewa wasu ma’aurata sun damfari gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawan kuɗi da adadinsu ya kai Dala miliyan 6.3 kan cinikin jirgi mai tashin angulu.

Kasancewar labarin na cigaba da yaɗuwa musamman a kafafen sada zumunta, kawo yanzu ba’a samu wani jawabi daga gwamnatin jihar kan batun wanda idan ƙarya ce, wakilan jaridar gwamnatin za su gaggauta yin gamsashshen bayani a kai domin kiyaye suka daga suka daga ƴan adawa.

Sannan, shuru da gwamnatin ta yi, mai yiwuwa akwai ƙamshin gaskiya a cikin rahoton wanda in da akasin haka ne, gwamnatin za ta shigar da jaridar ƙara.

People’s Gazette ta ƙara da cewa, mutanen biyu masu suna Ovi da Gloria Osazele ƴan kasuwan jiragen sama ne da ke zama a Legas inda su ke da kamfanin bada tallafin hayar jirgi mai tashin angulu waɗanda gwamnan ya saya ta hannunsu.

Kazalika, jaridar ta ce kasancewar gwamnan yana tsoron shiga komar hukuma, bai bayyana batun damfarar ba.

Sannan ya fara biyan Dala 250,000 a matsayin kuɗin dillanci inda bayan rabuwar ma’auratan, Ovi sai ya sauya sunan mallakar jirgin zuwa sunansa kamar yadda ta ruwaito. Daga nan sai ya fice zuwa ƙasar Amurka.

Bugu da ƙari, kasancewar ba a samu bayani daga ɓangaren gwamnan ko ma’auratan ba, haƙiƙanin bayanin al’amarin na ɗauke da sarƙaƙƙiya da ke buƙatar warwara.

By Babaji