
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Neja ta ƙaddamar da bincike akan zargin ɓullar wata cuta bayan wasu rahotannin cewa wani rashin lafiya ya yi ajalin wani yaro da kuma shafar ‘yan gidansu, inda aka yi kira ga al’umma da su kwantar da hankali da tabbatar da yi wa ‘ya’yansu rigakafi akai-akai.
Daraktan yaɗa labarai na Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Yunusa Sa’idu ne ya bayyana haka a wata takarda, inda ya ce gwamnatin ta yunƙura ne bayan mahaifin yaron ya yaɗa bidiyoyi a kafafen Soshiyal Mediya cewa wata cuta ta shiga cikin gidansa.
Da yake jawabi yayin ziyartar gidan mutumin, Daraktan Lafiyar Al’umma, Dakta Ibrahim Idris ya ce shiga tsakani na gwamnatin ya nuna yadda gwamnatin Gwamna Umaru Bago ke ƙoƙarin ganin ya bayar da kulawar lafiya ga mazauna a faɗin jihar.
Ya bayyana cewa, kowane rashi da ba san yadda ya kasance ba na da buƙatar bincike, don haka ne gwamnatin jiharta ƙudiri aniyar ɗaukar matakin bincike a kai.
A cewarsa, sanƙarau na ɗaya daga cikin halin da hukumomin lafiya suke la’akari da shi a irin wannan yanayi, yana mai ƙalubalantar masu zargi da cewa su yi taka-tsantsan har sai an fitar da sakamakon bincike a kai.
Dakta Idris ya kima shawarci iyaye da su ba wa jami’an lafiya haɗin kai yayin da ake gudanar da binciken musamman akan matakin kula da ‘ya’yansu
