Gwamnati ta raba murhun girki na zamani don rage gurɓacewar yanayi a Jihar Kaduna

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnatin Jihar Kaduna tare da haɗin gwiwar ma’aikatar muhalli ta gwamnatin Tarayya sun fara raba ingantattun murhun girki wa mazaunan jihar domin tabbatar da an inganta tsaftace muhalli da kiwon lafiya a jihar.

Kwamishinan Muhalli na jihar Abubakar Buba a ranar Talata a garin Kaduna ya ce gwamnati ta yi haka ne domin ganin ta rage matsalolin da ake fama da su yanzu na canjin yanayi da gurbacewar muhalli a jihar.

Ya ce raba wa mutane ingantacen murhun da gwamnati ta yi dabara ce da zai taimaka wajen rage matsalolin sare itattuwa, shakar gurbataccen iska, da rage fitar da iskar ‘carbon’ wanda ke fitowa a dalilin amfani da tsofaffin murhu.

Buba wanda shugaban fannin kuɗaɗe na ma’aikatar muhalli ya wakilce shi ya ce yin hakan na daga cikin dabarun da gwamnatin Uba Sani ya dauka domin inganta muhalli a jihar.

Ya ce wannan dabara zai taimaka wajen inganta muhalli, kawar da chanjin yanayi da inganta rayuwar mutane a jihar.

Shugaban fannin Kula da canjin yanayi na ma’aikatar lafiya ta Gwamnatin Tarayya Abdurrahman Bashir ya ce raba ingantattun murhun na daga cikin shirin Inganta muhalli da shima shugaban ƙasa Bola Tinubu ke yi a kasar nan.

Bashir ya tabbatar cewa amfani da tsofaffin murhu sun ci gaba da haifar da matsaloli da suka hada da gurbata iska da sare-saren itattuwa.

Bashir ya ce za a wayar da kan mutane mahimmancin amfani da murhun domin inganta lafiyar su da hana cutar da muhali.

Ya yi kira ga mutanen da suka samu murhun da su tabbatar sun yi amfani da su ta hanyoyin da suka kamata domin inganta lafiyar su da muhallin da suke ciki.

Nafisatu Bello daya daga cikin mutanen da suka amfana da wannan kyauta ta murhun ta shaida cewa amfani da murhun zai taimaka wajen rage shajar hayaƙi da kuma kudaden da suke kashewa wajen cefanan gida.

Ita kuwa Esther Anthony ta mika godiyarta ga gwamnati musamman yadda suka wayar da su kan illar shakar hayaƙi da zai iya kawo lahani ga lafiyar su.

By ukarofi