Gwamnatin Bayelsa ta nemi tallafin Bankin Heritage don ba wa matasa sana’a

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnatin jihar Bayelsa ta bayyana ra’ayinta na son ta haɗa hannu da Bankin Heritage don tallafa wa matasanta a vangaren sana’o’i da wasannin motsa jiki.

Mataimakin gwamnan jihar mai suna Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, ya bayyana haka ne yayin ziyarar ban girma tare da Kwamishinan matasa da wasanni, Daniel Igali da wasu zuwa ga mahukuntan bankin Heritage da suka kai Shalkwatar Bankin dake jihar Legas a kwanan nan.

Ewhrudjakpo ya bayyana cewa, a shirye yake da ya haɗa gwiwa da Bankin Heritage domin samar da abin yi ga matasa da kuma bunƙasa harkar wasanni domin ƙara samar musu da walwala da tattalin arziki.

Sannan kuma ya yaba wa bankin a kan irin rawar da ya sha takawa don ƙara bunƙasawa da gina matasa. Sannan tare da cusa musu aqidar sana’a don cigaban tattalin arziki.

Da yake mayar da nasa jawabin, Daraktan zartarwa na Bankin Heritage, Jude Monye, ya yi musu marhabin da zuwa. Kuma ya ba wa Mataimakin gwamnan tabbacin cewa bankin a shirya yake wajen tallafa wa gwamnatin jihar Bayelsa a vangarorin da ta zava.

Mista Monye ya ƙara da cewa, wannan mataki da bankin take a kai na tallafa wa matasan Nijeriya da sana’a da kuma a fagen wasannin ya nuna bankin tana da matuƙar shauƙin bunƙasa matasa don su zama mutane masu daraja a Duniya waɗanda za su goga kafaɗu da sauran masu manyan sana’o’i a ko’ina.

Daga ƙarshe, ya bayyana cewa, da ma Bankin Heritage yana gaba-gaba wajen tallafa wa duk wani ƙuduri mai kyau musamman idan ya shafi matasa da wasanni.

Sannan ya ƙara jaddada irin goyon bayan da Manajan bankin, Ifie Sekibo yake da shi a kan haɗa hannu da gwamnatin don samun nasarar shirin.

Sannan ya ƙara jaddada cewa, sun rungumi wannan shiri da yawun Manajan da masu ruwa da tsaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *