Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Yayin da ake ka-ce-na-ce tsakanin Gwamnatin Tarayya da wasu jihohi dangane da abincin da Gwamnatin tarayya ta raba wa jihohi, ita kuwa Jihar Jigawa ta ƙaddamar da rabon kayan abincin da ta karɓa daga hannun tarayya ɗin.
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya ƙaddamar da rabon kayan abincin a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, wanda ya ƙunshi buhuna 59,000 na shinkafa mai nauyin kilo 25, masara da sauran kayan abinci.
An fara rabon ga marasa galihun yau da kullum a mazaɓu 287 da ke faɗin jihar.
Da yake jawabi a Dutse lokacin rabon kayan abincin, Gwamna Namadi ya ce Gwamnatin Tarayya ce ta bayar da shawara tallafin domin kai ɗaukin agajin gaggawa ga al’ummar jihar.
Ya ce kayan abincin ya ƙunshi buhuna 13,825 na dawa, buhuna 9,500 na gero, buhuna 11,500 na masara da kuma buhuna 24,000 na shinkafa.
“Domin tabbatar da cewa tallafin ya isa gidaje da dama, gwamnatin jiha ta ƙara katan 23,000 na indomi, buhuna 5,000 na shinkafa, buhuna 500 na dawa, da kuma buhuna 5,000 na masara.” Inji Gwamna.
Kwamishina na musamman, Auwal ɗanladi Sankara, ya ce an zaɓo waɗanda za a raba wa tallafin daga dukkan mazaɓu 287 na faɗin jihar mai ƙananan hukumomi 27.
Ya ce rabon kayan tallafin ci gaba ne daga tallafin da Gwamnatin Umar Namadi ke bayarwa ga sama da mabuƙata miliyan uku a ɗaukacin jihar.
A wani labarin kuma Gwamna Namadi ya yi jaje da ta’aziyyar waɗanda ibtila’in ambaliya ya ritsa da su, ta hanyar asarar rayuka da waɗanda suka yi asarar dukiyoyi da kuma waɗanda suka rasa matsugunai.
