Gwamnatin Kamaru ta ƙaryata raɗi-raɗin mutuwar shugaban ƙasar Paul Biya mai shekaru 91 da aka daina jin ɗuriyarsa sama da wata guda tun bayan halartan taron Afirka da Chana.
Shugaba Paul Biya mai shekaru 91, ya bar ƙasar ne tun ranar 2 ga watan Satumba domin halartar taron Afirka da Chana da aka gudanar daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Satumba.
Tun daga lokacin ne aka daina jin ɗuriyarsa, inda hatta babban taron Majalisar ɗinkin Duniya da na ƙasashen Francophonie da ya saba halarta kuma aka sanar zai je ma, wakilci aka tura.
Haka zakalika, Paul Biya bai halarci wasan ƙarshe na gasar cin kofin Kamaru da aka gudanar kwanaki goma da suka wuce ba, kamar yadda ya saba yi.
Rashin halartan waɗandan taruka ya jefa ƴan ƙasar Kamaru cikin ruɗani, inda aka fara yaɗa jita-jita daga ciki da wajen ƙasar masamman a kofofin sada zumunta na zamani cewa shugaban ƙasar na cikin mawuyacin hali kwance awani abisiti a ƙasar Swizland.
Shiru da gwamnati da ma jam’iyyar RDPC mai mulki suka yi na dogon lokaci ya ƙara haifar da ruɗani a zukatan yan ƙasar, abin da ya sa ma wasu shugabannin jam’iyyun adawa suka buƙaci a bayyana musu halin da shugaban ƙasar ke ciki.
Cikin waɗanda suka fito fili suka buƙaci ƙarin haske kan halin da shugaba Paul Biya ke ciki, harda ficeccen lauya kuma ɗan takarar neman shugabancin ƙasar a jam’iyyar adawa Christian Ntimbane da ya rubuwata daraktan fadar shugaban ƙasar Samuel Mɓondo Ayolo wasiƙa.
Da yammacin wannan Talata, hukumomin ƙasar suka mayar da martani bayan da wata kafar yaɗa labarai ta yanar gizo da ke watsa shirye-shiryenta a ƙasashen waje ta sanar da mutuwar shugaban da ya kwashe shekaru 42 yana mulkin ƙasar.
Jacƙues Fame Ndongo, sakataren sadarwa kuma memba a jam’iyya mai mulki ne ya fara ƙaryata batun,
“Wannan labari ne marar tushe, don haka masu kishin ƙasa da abokan hulɗarmu ku kwantar da hankalinku.”
Sa’i kuma, babban sakataren jam’iyyar, Grégoire Owona, kuma ministan Kwadago, shi ma ya mayar da martani, ya na mai gargaɗin masu neman haifar da hargitsi.
“Waɗanda suke ƙoƙarin yaudarar jama’a ta hanyar sanar da mutuwar shugaban ƙasar Kamaru, za su girbi abin da suka shuka kan wannan ƙazafi.”
Daga bisani mai magana da yawun gwamnatin ƙasar kuma ministan sanarwa Rene Emmanuel Sadi ya ƙaryata zargin a hukumace, inda ya ce rahotannin da ake yaɗawa a kafofin sada zumunta tare da wasu tashoshin yaɗa labarai ba wani abu ba ne sai labarin ƙanzon kurege.
Mista Sadi ya ce shugaba Paul Biya na nan a raye cikin ƙoshin lafiya, saɓanin jita jitar da ake yaɗawa cewar ya mutu kuma yana cikin koshin lafiya.
