Gwamnatin Kano ta bayar da tallafi ga waɗanda gobara ta shafa a garin Zago

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙarƙashin ma’aikatar jin ƙai da rage talauci ta kai tallafi ga al’ummar da gobara ta shafa a garin Zago da ke ƙaramar hukumar Ɗanbatta.

Tallafin na kuɗaɗe da aka raba jiya a garin na Zago da ke ƙaramar hukumar Ɗanbatta ya kai jimillar Naira miliyan N6,576,537.33 an raba shi ga iyalai 28 da gobarar ta shafa a watan Fabrairu na shekarar 2025 da ta gabata.

Ta cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan al’umma a ma’aikatar jin ƙai da rage talauci Ibrahim Abdullahi ya rabawa manema labarai ta ce, a yayin rabon tallafin, babbar sakatariyar ma’aikatar, Hajiya Amina Yusuf ‘Yargaya, ta ce gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf tana matuƙar damuwa da duk wata matsala da ta shafi rayuwar al’umma, musamman waɗanda suka fuskanci bala’i.

Ta tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa al’umma a duk lokacin da irin wannan ƙalubale ya taso domin tabbatar da jin daɗi da walwalar jama’a, tana mai kira ga waɗanda suka amfana da su yi amfani da abin da suka samu ta hanyar da ta dace.

Shi ma da yake jawabi, sakataren zartarwa na hukumar agajin gaggawa ta Jihar Kano (SEMA), Abdullahi Isyaku Kubarachi ya bayyana cewa an gudanar da binciken tantance girman asarar da gobarar ta afku kafin a samar da tallafin.

Ya roƙi mutane da su rinƙa kashe wuta bayan gama aikin gida musamman da dare kafin su kwanta, yana mai tabbatar da cewa SEMA za ta ci gaba da aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki domin taimakawa al’umma a duk lokacin da bala’i ya auku.

Kazalika, mashawarcin gwamna na musamman kan ayyukan jin ƙai Dakta Garba Ibrahim ya buƙaci al’umma da su rinƙa yin taka-tsantsan don kaucewa afkuwar gobara, yana mai jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaba da taimakawa duk wanda bala’i ya shafa.

A nasa ɓangaren, babban nataimaki na musamman ga gwamnan Jihar Kano kan tallafin al’umma, Muttaƙa Sani Gaya ya tabbatar da shirin gwamnatin Kano na ci-gaba da kula da walwalar al’umma, musamman masu rauni da waɗanda bala’i ya shafa.

Da yake bayyana farin cikinsa da tallafin, shugaban ƙaramar hukumar Ɗanbatta, Jamilu Abubakar Ɗanbatta wanda Abdulƙadir Muhammad ya wakilta, ya gode wa gwamna Abba Kabir Yusuf, yana mai cewa ba shakka taimakon zai taimaki waɗanda abin ya shafa wajen rage musu dukiyar da suka yi asara.

Waɗanda suka amfana da tallafin sun nuna godiyarsu ga gwamnatin Kano bisa tallafin da aka kawo musu a lokacin da suka fi buƙata.

By ukarofi