Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi gargaɗin cewa mutanen da suka sare bishiya ba tare da izini ba za su fuskanci hukunci a jihar.
Wannan matsaya mai muhimmanci wani ɓangare ne na babban shiri na kiyaye muhalli da yaƙi da sauyin yanayi.
An sanar da hakan ne a yayin taron dashen itatuwa na shekarar 2024 da aka gudanar a unguwar Khalifa Isyaku Rabiu da ke Kano.
Gwamna Yusuf ya jaddada cewa shirin na dasa itatuwa sama da miliyan 3 a faɗin jihar, inda ya jaddada muhimmancin rawar da itatuwa ke takawa a rayuwar bil’adama ta hanyar inganta iska, samar da inuwa, da kuma tallafa wa halittu.
Ya kuma jaddada muhimmancin shigar da al’umma cikin wannan shiri na muhalli, inda ya yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu, ƙungiyoyin farar hula, da ɗaiɗaikun jama’a da su goyi bayan ƙoƙarin gwamnati na samar da yanayi mai inganci da lafiya a Jihar Kano.
Shi ma mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga jama’a da su dasa itatuwa a gidajensu.
Ya tuno da tsananin zafi da aka samu a jihar a shekarar da ta gabata, inda ya nuna wajibcin ƙara itatuwa don rage matsananciyar yanayi.
Bugu da ƙari, kwamishinan muhalli da sauyin yanayi, Alhaji Nasir Sule Garo, ya bayyana muhimmancin dashen itatuwa wajen yaƙi da sauyin yanayi da tabbatar da kwanciyar hankali.
Ya bayyana cewa bishiyoyi su na da muhimmanci wajen ƙara yawan iskar da a ke shaƙa, hana zaizayar ƙasa, da kuma kiyaye daidaiton muhalli.
