Gwamnatin Kano ta janye dokar hana bin wasu tituna ga matuƙa baburan adaidaita sahu

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Gwamnatin jihar Kano ta janye dokar taƙaita bin hanyoyin ga matuka babura masu kafa uku da aka fi sani da Adaidaita sahu a wasu titunan Kano,

Shugaban Hukumar Karota Baffa Babba Ɗan agundi ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gabatar a ofisoshin sa.

Ya ce “mun janye dokar ne saboda biyayyar da ‘yan adaidaita suka yi ga dokar da kuma yadda al’umma suka koka akan ta.”