
A ƙoƙarinta na cigaba da ayyukan jinƙai da kyautata rayuwar al’umma ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf na, Gwamnatin Jihar Kano na cigaba da kai ziyara ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar waɗanda za su rabauta da baƙoncin gwamnan domin tattauna matsaloli da bijiro da hanyoyin magance su.
A sanarwar da Jami’ar Yada Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa Manema Labarai, Shugaban Karamar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Mai Fata ne ya bayyana haka, jim kadan bayan kaddamar da rabon babura guda hamsin (50) kyauta ga jama’ar yankin a sakatariyar ƙaramar hukumar.
Shugaban karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata ya bayyana wannan shi ne karo na uku (3) da ake raba babura kyauta ga wadanda suka cancanta, kama daga kan matasa da magidanta da kuma malamai.
“Akwai abubuwa da dama da za su zo daga jiha, mai girma Gwamna a shirye yake na a taimaki al’uma. Ko jiya an yi taro an yaye wasu mutum dubu biyu da dari shida 2600 da suka rabauta da abubuwan alheri, wani ma ya ce an ba shi waya. Don haka duk abin da ya taso idan ka ga an ba wani wani abu, idan ka yi hakuri ka yi murna tare da jin dadi a zuciyarka, kila kai ne a gobe.” Alhaji Hamza Sule Mai Fata.
Da yake jawabi, Sakataren Kokas na yankin, Alhaji Ahmad Haruna, wanda ya yi magana a madadin Jagoran NNPP ta yankin, Alhaji Ahmad Garba Bichi, ya bayyana wasu da yawan aikace-aikacen da Majalisar karamar hukumar ta yi, inda ya hakurkutar da wadanda wannan kabakin alherin bai kai gare su ba ta hanyar yi musu albishir na tagomashin da gwamnati ta shirya wa al’umma a gaba.
“Bayan wannan kuma, akwai empowerment na mutane da yawa da aka shirya za a ba wasu jari na kudi, saboda haka ina so na jawo hankalin jama’a babu abin da za a iya yi a kokaci guda, a hankali a hankali muna tahowa in sha Allahu kowa abin da Allah ya kadarta rabonsa ne zai same shi, a kara hakuri.” Sakataren Kokas Alhaji Ahmad Haruna.
Waɗannan mutane dai hamsin (50) da suka amfana da kyautar baburan, sun yi matukar godiya gami da nuna tsantsar farin cikinsu, inda daya daga cikinsu, Sani Habibu ya yi magana a madadinsu.
“Yau rana ce ta farin ciki wanda kowa ya sani wadanda aka ba wannan baburan har ga Allah a shekaran jiya ba su san za a ba su ba, amma cikin ikon Allah jiya da daddare kowa aka yi masa albishir, wannan abu sai dai mu ce, Allah ya saka da alheri, amin.” Sani Habibu.
Haka bangaren mahalarta taron, da yawa jiga-jigan ma’aikatan yankin tare da manya baki sun tofa albarkacin bakinsu wajen fatan alheri ga wannan gwamnati, da suka hadar da; Mataimakin Shugaban karamar hukumar, Sakataren Mulki, Daraktan Mulki, Shugaban Jam’iyya, Sakataren Kokas, mai bai wa Shugaban Majalisar yankin shawara a kan harkokin siyasa da sauransu.






