Gwamnatin Kano za ta raba kayan makaranta kyauta

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na shirin raba kayan makaranta ga ɗalibai sama da 789,000 a makarantun firamare na gwamnati a faɗin jihar domin magance matsalar yaran da basu zuwa makaranta.

Taron wanda aka shirya yi a ranar Litinin 13 ga watan Junairu, 2025, da ƙarfe 1:00 na rana a ɗakin taro na Coronation da ke gidan gwamnatin Kano, tallafin ya shafi ɗaliban ajin firamare 1 a makarantun gwamnati 7,092 dake faɗin ƙananan hukumomin 44.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana haka inda yake cewa “Wannan gwamnatin ta ƙudirin aniyar rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Kano tare da bai wa iyaye marasa galihu tallafin da suke buƙata domin biyan buƙatun ‘ya’yansu”.

Waiya ya ƙara da cewa “Wannan karimcin ya nuna jajircewarmu na tabbatar da cewa ilimi ba gata ne kawai ba, haƙƙi ne na kowane yaro a Jihar Kano.”

Shirin na neman ƙarfafa gwiwar shiga makarantu da kuma rage ƙalubalen kuɗi da iyaye ke fuskanta wajen bai wa ‘ya’yansu ilimi na asali.