Gwamnatin Katsina ba ta da iko da DSS ko jami’an tsaro – Maiwada Ɗan Malam

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnati a bisa tsarin mulkin Nijeriya ba ta da iko akan jami’an tsaro da DSS Inji Maiwada Dan Malam Darakta Janaral kan yaɗa labarai na gwamnan jihar Katsina.

Ɗan Malam ya maida martani ne akan zargin da Ahamed Saleh Junior wanda ya nemi tsayawa takarar kujerar majalisar wakilai na mazaɓar ƙananan hukumomin Mani da Bindawa ƙarƙashin jam’iyar APC.

Saleh Juniya ya zargi gwamnatin Katsina da sanya a tsare shi har sai da aka kammala zaɓen fidda yan takara na jam’iyar a mazaɓar Mani da Bindawa.

DG Ɗanmalam ya bayyana cewa DSS hukumar ce da take ƙarƙashin gwamnatin tarayya wanda alhakin ta ne ta tabbatar da anbi doka da Oda haka kuma ta bincika duk wani lamari ta take gani na barazana da tsarin ƙasa da ɗaukan mataki nan take.

Ya ce duk da cewa Gwamna shine babban jami’in tsaro na ɗaya a jihar hakan ba shine zai sa ya shiga aikin hukumar DSS na abinda ya shafi tsaro a jihar ba kuma hukumar ce ta fi dacewa ta faɗi ainihin dalilin da yasa hukumar ta tsare ɗan takarar.

“Maimakon ayi ta yayata zarge zargen da ɗan takarar ya yi yakamata yan jarida su tambaye sa daliln da sa DSS ta tsare shi,”Inji Maiwada Ɗanmalam,

Hajiya Jamila Abdu Mani tayi takara da shi inda ta sami nasarar samun tikitin shiga takarar kujerar majalisar wakilai a mazaɓar Mani da Bindawa ƙarƙashin jam’iyar APC a jihar Katsina.

By ukarofi