Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin jihar Katsina ta mayar da martani kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin wasu ‘yan bindiga da suka tuba da kuma hukumomin jihar.
A yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Litinin, kwamishinan harkokin tsaro na cikin gida na jihar Katsina, Nasir Mu’azu, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba ta tattaunawa da ‘yan bindiga ba.
A ƙarshen makon da ya gabata, Ado Aleru, wani shugaban ‘yan bindiga da hukumomi ke nema ruwa a jallo, ya bayyana a wani taron zaman lafiya da aka gudanar a garin Bichi, ƙaramar hukumar ɗanmusa ta jihar Katsina.
Aleru, wanda tun daga shekarar 2020 ke cikin jerin sunayen masu laifi da rundunar ‘yansanda ke nema, kuma aka sanya kyautar naira miliyan 5 ga duk wanda ya kama shi, an gan shi a wani bidiyo yana jawabi ga al’ummar gari, jami’an gwamnati, jami’an tsaro da kuma shugabannin gargajiya.
Wasu daga cikin shugabannin ‘yan bindiga sun mika wuya tare da rungumar zaman lafiya a yayin taron.
A ‘yan kwanakin nan, an gudanar da irin wannan taron zaman lafiya da ‘yan bindiga a wasu kananan hukumomi, ciki har da Jibia.
Mu’azu ya ce ko da yake gwamnatin jihar ba za ta shiga tattaunawa da ‘yan bindiga ba, za ta ba su damar komawa cikin al’umma yadda ya kamata muddin suka ajiye makamansu.
Kwamishinan ya bayyana cewa wasu al’ummomi daga Jibia, Batsari, da ɗanmusa sun gudanar da tattaunawa mai ma’ana da wasu daga cikin ‘yan bindigar da suka tuba.
