Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, ya magantu game da rikicin da ke cikin masarautar Zazzau, inda ya bayyana cewa tsohon Wazirin Zazzau, Ibrahim Muhammad-Aminu, ya daina zuwa aiki watanni bakwai kafin gwamnati ta tsige shi daga muƙaminsa.
Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da Shugaban Yankin Kaduna na Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), Bashir Rabe-Mani, da Shugaban Yankin Kaduna na Media Trust Group, Yusuf Jidda, suka kai masa ziyara a Zariya.
Bamalli ya ce tsohon Waziri ya dakatar da zuwa aiki tsawon watanni bakwai kafin a fitar da sanarwar korar sa daga gwamnati.
Ya ce majalisar sarakunan ta tura wani kwamiti da ya ƙunshi mambobinta gaba ɗaya ƙarƙashin jagorancin Nuhu Aliyu-Magaji, Galadiman Zazzau, domin su gana da Muhammad-Aminu kan dalilin rashin zuwansa aiki.
Ya ƙara da cewa tsohon Waziri ya shaida wa wakilan cewa zai dawo aiki, amma hakan bai faru ba.
“Bayan wani lokaci, na sake tura su domin su gana da shi, amma bai bada wata amsa ba.
“Saboda haka, ban da wani zabi illa rubuta wa gwamnatin jiha takarda kan lamarin, daga baya ne aka sanar da tsige shi daga mukamin,” inji Bamalli.
“Abin takaici, wasu kafafen yada labarai sun bayyana lamarin a wata fuska daban; wasu ma sun kai ga nuna cewa tsohon Waziri an zalunce shi ko kuma an bi shi da kiyayya,” inji shi.
Duk da hakan, Sarkin ya ce ko da yake an samu kura-kurai a tsarin zaben sabon Sarkin Zazzau, ya ce yana alfahari da masu zaben sarki (kingmakers), kodayake ba wanda ya kada kuri’a a kansa.
Ya ce yana sa ran wasu mutane, musamman ‘yan jarida, za su zurfafa bincike don gano hakikanin yadda aka gudanar da zaben Sarkin Zazzau a shekarar 2020.
A cewarsa, zaɓen ya gudana ne a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, ƙarƙashin kulawar tsohon Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), wanda yanzu shi ne Ministan Muhalli, Balarabe Abbas.
Sarkin ya ce a lokacin, kwamishinan ‘yan sanda da daraktan DSS suma sun kasance masu sa ido a wajen gudanar da zaɓen.
