Gwamnatin Katsina za ta gina wa ‘yan gudun hijira gidaje 152 a Jibiya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 

Gwamnatin jihar Katsina tare da Hukumar Bunƙasa Tattalin Arziki na Majalisar ɗinkin Duniya (UNDP) za su gina wa ‘yan gudun hijira gidaje guda 152 a ƙaramar hukumar Jibiya.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana haka a garin Jibiya lokacin da ya ke aza harsashi gina gidajen.

Ya ce mutanen da suka rasa gidajen su da wurin sana’o’in su ne  gwamnati za ta gina masu gidajen tare da basu kuɗaɗen da za su fara kasuwanci. 

Haka kuma gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin za ta samar da fitillu masu amfani da hasken rana da kuma wurin gudanar da kasuwanci a unguwar gidajen.

Malam Dikko Raɗda ya bayyana cewa gwamnatin ta zaɓo mutane 2,000 da suka fito daga ƙananan hukumomi 8 da taadanci ya shafa da za ta basu kuɗaɗen da za su fara sana’a.

Gwamnan sai ya umurce ‘yan kwangila da za su aikin gina gidajen da su sayi kayan aikin ginin a nan garin Jibiya tare da ɗaukar ma’aikata daga nan garin na Jibiya.

By ukarofi