Gwamnatin Katsina za ta mayar da cibiyoyin shan magani zuwa manyan asibitoci a jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina
za ta cigaba da ɗaukaka cibiyoyin shan magani zuwa manyan asibitoci a faɗin jihar.

Kwamishinan harkokin lafiya Hon Musa Adamu Funtua ya faɗi haka da yake ƙarin haske akan rangadin da gwamna Dikko Raɗɗa ya kai akan hukumomi ƙarƙashin ma’aikatan kiwon lafiya na jihar.

Ya ce gwamnatin jihar ta fara mayar da cibiyar kiwon lafiya a Faskari da Zango akan kuɗi Naira miliyan 599.

Haka kuma ta fara gudanar da irin wannan aiki a Charanchi da Ɗandume akan kuɗi Naira biliyan 3.

Kwamishinan ya kuma sanar da cewa majalisar zartarwa ta jihar ta amince da faɗaɗa tare da ɗaukaka wasu ƙananan asibitoci guda 150 domin samun ingantaccen kulawa ta fannin lafiyar su a faɗin jihar.

Hon Adamu Funtua yayi kira ga al’ummar jihar da su tashi tsaye wajan sa ido da kulawa ga waɗannan gine gine na gwamnati.

Ya kuma jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na inganta harkar kiwon lafiya a faɗin jihar.