Gwamnatin Katsina za ta sayi ton 20,000 na takin zamani a daminar bana

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamishinan noma Lawal Aliyu Shargalle ya faɗawa manema labarai haka a Katsina bayan kammala taron majalisar zartarwa na jihar .

Wasu abubuwan da majalisar zartarwar ta amince da su sun haɗa da tsarin shaidar dijital, da inganta asibitocin farko, tare da gyaran harkar kayan aikin noma.

Ta kuma amince da ɗaukar ma’aikatan lafiya, samar masu da wutar lantarki ta hasken rana da babura masu ƙafa uku ga cibiyoyin lafiya na PHC guda 229.

A kan kasafin kuɗin shekarar da ta wuce kamar yadda kwamishinan yaɗa labarai Dr Salisu Bala Zango ya faɗi, jihar Katsina ta samu kashi 81.66% na kuɗaɗen shiga, tare da aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa.

Dr Zango ya bayyana cewa majalisar zartarwa ta Jihar ta amince da muhimman manufofi da tsare-tsaren raya ƙasa da nufin ƙarfafa harkar noma, inganta isar da ayyukan kiwon lafiya, bunƙasa mulki ta hanyar dijital, da kuma hanzarta bunƙasar ababen more rayuwa da tattalin arziki a faɗin jihar.

Ya yanke waɗannan shawarwari ne a yayin zama na biyu na yau da kullum na Majalisar Zartarwa ta Jihar Katsina na shekarar 2026, wanda aka gudanar a babban ɗakin taro na gidan Janar Muhammadu Buhari da ke Katsina, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan jihar Malam Dikko Raɗɗa.

Kwamishinan ya ce shawarwarin da majalisar ta aminta da su,sun nuna ƙudirin gwamnatin jihar na ganin an kawo wa al’umma ribar dimokiraɗiyya kai tsaye, bisa tsarin Building Your Future Agenda.

Kwamishinan noma, Alhaji Aliyu Lawal Shargalle, ya bayyana cewa majalisar ta amince da sayen tan 20,000 na taki, wato buhuna 400,000 na takin NPK da Urea, domin noman damina na shekarar 2026.

Ya ce wannan shiri na da nufin tabbatar da samuwar ingantattun kayan noma a kan lokaci ga manoma, a farashi mai rahusa, domin ƙara yawan amfanin gona, tabbatar da wadatar abinci, da inganta rayuwar al’ummomin karkara a faɗin jihar Katsina.

Dangane da kayan aikin noma, ya bayyana cewa majalisar ta duba sabon tsarin amfani da kula da taraktoci da sauran kayan aiki a cibiyoyin aikin noma da ke ƙananan hukumomi 34 na jihar. Ya ce zuwa yanzu, taraktocin sun noma fiye da hekta 7,000 ga manoma.

Akan haka ne, majalisar ta amince da matakan ƙara tsaro ga kayan aikin da kuma faɗaɗa damar manoma su amfana da su a farashi mai sauƙi.

A ɓangaren sauya fasalin dijital, Darakta Janar na KATDICT, Malam Naufal Ahmed, ya ce majalisar ta amince da tsarin iKatsina Framework a matsayin ginshiƙin tsarin ayyukan dijital na gwamnati a jihar.

Ya bayyana cewa tsarin iKatsina Digital Resident Identification System zai samar da tsari guda ɗaya, mai tsaro, da zai bai wa ‘yan jihar damar samun ayyukan gwamnati a dukkan ma’aikatun MDAs. Wannan, a cewarsa, zai ƙara inganci, gaskiya da amfani da bayanai wajen tafiyar da mulki, tare da sauƙaƙa isar da ayyuka ga al’ummar Katsina.

By ukarofi