Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin jihar Legas ta naɗa mai tasiri a shafukan sada zumunta, Ayomiposi Oluwadahunsi, wacce aka fi sani da Mandy Kiss, a matsayin jakadiyar ƙungiyar Kick Against Drug and Substance Abuse initiatiɓe (LASKADA).
Kwamishinan matasa da ci gaban al’umma, Mobolaji Ogunlende ne ya sanar da naɗin a yayin wani taron LASKADA a ranar Talata.
Ogunlende ya ce manyan magoya bayan Mandy Kiss da kuma tasiri a tsakanin matasa ne suka sanar da matakin, inda ya ce jihar na neman sabbin hanyoyin da za a daƙile ƙaruwar al’amuran da suka shafi shaye-shaye.
“Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi wata cuta ce da ta shafi lungu da saƙo, da al’ummarmu, da al’ummominmu, gwamnati ba za ta iya yakar ta ita kadai ba, dole ne mu hada kai da mutanen da za su iya kaiwa ga talakawa, kuma Mandy Kiss, mai mabiya sama da 400,000, ta dace da wannan rawar,” inji shi.
Kwamishinan ya ba da wannan aiki a hukumance ga masu yin tasiri, inda ya buƙaci matasa da su shiga yaƙin da ake yi da miyagun ƙwayoyi.
Naɗin na zuwa ne kwanaki bayan Mandy Kiss ta jawo suka a shafukan sada zumunta game da kalamanta mai cike da cece-kuce game da “jima’i na marathon.”
