Likitoci 11,000 ne ke kula da lafiyar ‘yan Nijeriya miliyan 240 – NARD

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Likitoci ta Nijeriya (NARD) ta nuna fargaba kan yadda ƙasar ke ƙara shiga taɓarɓarewar harkar likitanci, inda ta bayyana hakan a matsayin “haɗari,” yayin da ta sanar da sabbin matakan kare martabar likitoci da tabbatar da ingantaccen kiwon lafiya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba don bikin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai, NARD ta koka da cewa a halin yanzu kowane likita a Nijeriya yana kula da marasa lafiya 9,083, adadin da ta ce ya banbanta da tsarin duniya.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun shugaban NARD, Dr. Mohammad Suleiman; Babban Sakatare, Dr. Shuaibu Ibrahim; da Sakataren Watsa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Dr. Abdulmajid Ibrahim, ta kuma bayyana cewa likitocin da ke zaune a duk faɗin ƙasar, daga ranar 1 ga Oktoba, 2025, za su daina aiki fiye da sa’o’i 24.

Nijeriya dai ta kwashe shekaru tana fama da matsananciyar ƙarancin likitoci, lamarin da ya yi ƙamari sakamakon hijirar su zuwa ƙasashen ƙetare. A cewar Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Pate, sama da likitocin Nijeriya 16,000 ne suka bar ƙasar a cikin shekaru biyar zuwa bakwai da suka gabata domin neman ingantacciyar yanayin aiki a ƙasashen waje.

Wannan batu ya rage adadin likitoci mazauni ƙasa zuwa 11,000 kacal don kula da al’ummar ƙasar sama da mutane miliyan 240, abin da ya haifar da murƙushe aikin da NARD ta ce yana barazana ga marasa lafiya da likitoci su kansu.

ƙungiyar ta bayyana ƙididdiga mai ban tsoro game da lokutan aiki a asibitocin Nijeriya: likitoci masu neman ƙwarewa suna aiki da matsakaicin awa 106.5 a kowane mako kuma masu tiyata suna aiki kamar awa 122.7 a mako-mako.

NARD ta yi gargaɗin cewa irin aiki fiye ƙa’ida ba makawa yana haifar da gajiya da ƙara kura-kuran likita, jefa marasa lafiya cikin haɗari da tura likitoci cikin wani yanayi na gajiyar ƙwaƙwalwa

“Wannan yanayin abin matuƙar damuwa ne. Sau da yawa, likitocinsuna sadaukar da lafiyarsu, wani lokacin kuma suna sadaukar da rayuwarsu, don yi wa majinyata hidima. Amma tambaya mai raɗaɗi ita ce: Wa zai kula da iyalansu da waɗanda suka dogara da su bayan mutuwarsu?”.

A cikin abin da aka bayyana a matsayin “matakin kiyaye kai”, NARD ta ayyana cewa likitoci masu neman ƙwarewa ba za su sake ɗaukar hidimar da ta wuce sa’o’i 24 ba, suna masu dagewa cewa dole ne a sami lokacin hutu na wajibi bayan kowane likacin aiki.

By ukarofi