Gwamnatin mu na iya ƙoƙarin ta wajen tallafa wa addini – Gwamna Raɗɗa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Katsina malam Dikko Raɗɗa ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da inganta jituwa tsakanin addinai, zaman lafiya da haɗin kan ruhaniya, inda ya bayyana tarukan addini kamar mauludin ƙasa na Shehu Ibrahim Inyass na shekarar 2026 a matsayin muhimman dandali na gyaran ɗabi’a, ƙarfafa zumunci da samar da zaman lafiyar ƙasa.

Ya bayyana hakan ne jiya yayin liyafar cin abincin dare da gwamnatin jihar ta shirya domin mahalartan mauludin ƙasa na 2026, wadda aka gudanar a babban zaure na Banquet Hall, gidan gwamnati, Katsina.

Taron ya samu halartar shugabannin Tijjaniyya, malamai, sarakunan gargajiya da sauran manyan baƙi.

“Wannan taro alama ce ta ibadarmu ga Allah da kuma nauyin da ke kanmu na ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’ummarmu. Kasancewar fitattun malamai da mabiya Ɗarikar Tijjaniyya a Katsina albarka ce kuma abin alfahari ga jiharmu,” in ji Gwamna Raɗɗa.

Gwamnan ya nuna godiya ta musamman ga iyalan Tijjaniyya bisa zaɓar Jihar Katsina a matsayin mai masaukin mauludin ƙasa na tarihi na 2026, yana mai cewa hakan ya nuna amincewa da yanayin zaman lafiyar jihar, kyakkyawar tarbarta da kuma gadon addinin Musulunci da take da shi.

“Muna matuƙar godiya ga iyalan Tijjaniyya bisa kawo wannan mauludin ƙasa na tarihi zuwa Katsina.

Ya bayyana ladabi, haɗin kai da ’yan’uwa da mabiya suka nuna a duk tsawon taron sun nuna ingantattun koyarwar Musulunci da kuma gadon Shehu Ibrahim Inyass mai ɗorewa,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma yi kira ga malamai da al’ummar Musulmi da su ci gaba da sanya Jihar Katsina da ƙasar nan cikin addu’o’insu.

“Muna buƙatar addu’o’inku na dindindin domin jiharmu da ƙasarmu. Sai da taimakon Allah kaɗai za mu iya shawo kan ƙalubalenmu, na tabbatar da zaman lafiya, tare da samar wa al’ummarmu kyakkyawar makoma,” in ji gwamnan.

Ya ƙara da cewa tarukan addini na da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa zumunci da tabbatar da zaman lafiya a tsakanin jama’a.

“Gwamnatin mu za ta ci gaba da tallafa wa ayyukan addini da ke inganta zaman lafiya, haƙuri da haɗin kai.

Malam Dikko yace zaman lafiya ba wai ana gina shi ne kawai ta manufofi da hukumomi ba, ana gina shi ne ta imani, addu’o’i na gaskiya da kuma haɗin kan zukatan jama’a,” in ji gwamna Raɗɗa.

A baya, Khalifa Mahi na Shehu Ibrahim Inyass, wanda Sheikh Muhammadul Ƙuraish Sheikh Ibrahim Inyass ya wakilta, ya bayyana godiya ga gwamnatin Jihar Katsina bisa kyakkyawar tarba da karamcin da aka nuna wa tawagar.

“Muna matuƙar godiya bisa girmamawa, mutunci da alherin da gwamnatin jihar Katsina da al’ummarta suka nuna mana. Wannan ya nuna ƙwazon gwamna wajen tallafa wa ilimin addinin Musulunci da kuma haɗin kan al’ummar Musulmi,” in ji shi.

Haka nan, Shugaban ƙungiyar Tijjaniyya na ƙasa, Sheikh Ahmad Tijjani Awwal, ya yabawa gwamnatin jihar bisa tallafin na kayan aiki da ta bayar, yana mai bayyana nasarar gudanar da Mauludin a matsayin shaida ta shugabanci nagari da kyakkyawar haɗin gwiwa.

Shi ma Shugaban Kwamitin shirya taro na Jihar Katsina, Sheikh Hadi Balarabe, ya nuna godiya ga Gwamna Raɗɗa bisa yadda ya nuna cikakken goyon baya ga taron tare da tabbatar da cewa an tanadi dukkan shirye-shirye yadda ya dace.

Sauran manyan malamai, ciki har da Gwani Munnir Sheikh Jafar Katsina, sun gabatar da addu’o’i da shawarwari, inda suka ƙarfafa al’ummar Musulmi da su ci gaba da tsayawa kan tafarkin zaman lafiya, haɗin kai da biyayya ga Allah.

By ukarofi