Gwamnatin Nijeriya ta jinjina wa Saudiyya bisa samar da gurbin karatu ga ɗalibai 50 a fannin man fetur

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnatin Tarayya ta jinjina wa Masarautar Saudiyya bisa samar da gurbin karatu na kyauta ga daliban Nijeriya su 50 domin karantar fannin man fetur da ma’adanan kasa.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi baƙuncin Jakadan Saudiyya a Nijeriya, Yousef Bin Mohammed Al-Balawi, wanda ya ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja ranar Litinin, 27 ga watan Afrilu, 2026.

Ministan ya bayyana cewa wannan tallafin karatu ya zo daidai da burin gwamnati na bunkasa ilimi da kwarewa a fannonin da suka shafi tattalin arzikin kasa. Ya ce wannan ba gurbin karatu ba ne kawai, a’a, wani babban jari ne da za a zuba wa matasan Nijeriya.

“Wannan mataki zai samar da kwararrun da Nijeriya ke bukata a masana’antun man fetur da ma’adanan ƙasa,” inji Ministan. 

Ya kuma ƙara da cewa an tsara shirin ta yadda dalibai 50 za su rika amfana a duk shekara, wanda hakan zai tabbatar da ɗorewar shirin na dogon lokaci.

A nasa ɓangaren, Jakada Al-Balawi ya sanar da cewa gurbin karatun ya fito ne daga Jami’ar Man Fetur da Ma’adanai ta King Fahd (KFUPM). Ya bayyana cewa tallafin ya hada da Biyan kuɗin makaranta (Tuition), Tikitin jirgin sama na zuwa da dawowa, Wajen kwana kyauta, da Alawus ɗin dake shiga hannu a kowane wata.

Jakadan ya jaddada cewa wannan ƙoƙari na nuna kyakkyawar alaƙar dake tsakanin ƙasashen biyu, yana mai cewa Saudiyya da Nijeriya ginshikan tattalin arziki ne a yankunansu waɗanda ke da damar bunƙasa hulɗar kasuwanci a tsakaninsu.

Ministan ya kuma yi amfani da damar wajen bayyana jimamin Nijeriya game da taƙaddamar dake faruwa a yankin tekun Gulf, inda ya miƙa saƙon goyon bayan Nijeriya ga ƙasar Saudiyya.

Ya bayyana fatan samun zaman lafiya da kuma daidaita duk wata matsala ta hanyar diflomasiyya.

A ƙarshen zaman, Ministan ya tabbatar wa jakadan cewa Nijeriya za ta gaggauta aiwatar da sauran yarjeneniyoyin da aka kulla da Saudiyya, ciki har da wadanda suka shafi fannin yada labarai da sauran sassa.

Ziyarar ta samu halartar Babban Sakataren ma’aikatar, Dr. Binyerem C. Ukaire, da wasu manyan daraktoci na ma’aikatar yada labaran.

By ukarofi