Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da shirin fara rabon bishiyoyi guda miliyan 10 da ta ke raino ga al’ummar jihar domin dasawa a muhallan su.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir Muhammad Hashim ne ya baiyana haka yayin da ya kai ziyarar gani-da-ido ga wuraren rainon bishiyun a ƙananan hukumomin Gwarzo da Dawakin-Kudu.
A cewar Hashim, bishiyoyin da ake raino kuma ,a a raba sun haɗa da zogale, ɗorawa, lemon tsami, malmo, mangwaro, lemon zaƙi da goba da sauran su.
Kwamishinan ya ce za a raba su ga al’umma domin kowa ya dasa a mahallin da don samun muhalli mai lafiya da tsafta da nagarta.
“Bisa jagoranci da kuma sahalewar Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na dasa bishiyoyi miliyan goma a wannan shekarar, na kai ziyarar aiki zuwa wasu daga cikin wuraren rainon bishiyoyi a Gwarzo da Dawakin Kudu.
“A wannan wajen raino muna da bishiyoyi irin su zogale, ɗorawa, lemon tsami, malmo, mangwaro, lemon zaƙi da goba wanda muke sa ran zamu rabar domin dasawa a sassa daban daban na Jihar Kano,” inji Hashim.
Kwamishinan ya yi kira ga ‘ kungiyoyin al’umma da makarantu da su cike fom din da za a raba nan gaba ko su rubutowa Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi don samun wannan bishiyoyi domin shukawa.
