Ndume ya yaba wa Tinubu kan amincewa da biliyan N68 don inganta wutar lantarki a Maiduguri

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, ya yabawa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da tallafin kudi na Naira biliyan 68 domin gudanar da aikin Tashar Wutar Lantarki a Maiduguri (MEPP).

Za a fitar da kuɗin ne daga watan Maris 2026 zuwa Disamba 2028, domin magance karancin wutar lantarki a Jihar Borno, matsalar da hare-haren ‘yan ta’adda suka ƙara ta’azzara ta hanyar lalata muhimman injinan rarraba wutar.

Ndume ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Litinin, inda ya ce samun tsayayyar wutar lantarki zai bunƙasa harkokin tattalin arziki, taimaka wa ƙanana da matsakaitan ‘yan kasuwa, tare da taimakawa kokarin soja wajen yaki da ‘yan ta’adda.

Ndume ya kuma bukaci hukumomin tarayya da na jiha, rundunar soja da kuma al’umma gaba daya su tabbatar da cewa ba a sake lalata kayayyakin wutar lantarki ba, ko daga ‘yan ta’adda ko kuma masu barna.

Ya ƙara jaddada cewa ya kamata jama’a su rika kare kayan wutar lantarki tare da taimaka wa jami’an tsaro wajen hana barnata s

By ukarofi