Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Kula da Aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON) ta ware ranar 23 ga watan Mayu, 2026 a matsayin ranar tashin jirgin farko na maniyyatan Hajjin shekarar 2026.
NAHCON, a cikin wata sanarwa da Fatima Sanda Usara, Mataimakiyar Darakta a Sashen Yaɗa Labarai da Bayani ta fitar, ta bayyana cewa jirgin farko zai tashi ne daga Filin Jirgin Sama na Gateway International Airport da ke Abeokuta, Jihar Ogun, ta jirgin kamfanin jiragen FlyNas.
Ta ce wannan shi ne karon farko da alhazan Jihar Ogun za su fara tashi daga sabon filin jirgin da ke babban birnin jihar, bayan kammala gina shi.
A cewar sanarwar, a ranar za’a samu wasu tashin jirage kamar haka, Umza da Maɗ Air daga Abuja, dauke da alhazan jihohin Kogi da Nasarawa.
Sai kuma jirgin Air Peace daga Lagos, dauke da alhazan Jihar Oyo sannan kuma wani jirgin FlyNas zai tashi daga Birnin Kebbi.
NAHCON ta ce ma’aikatan ta, ciki har da ma’aikatan wucin-gadi na tawagar lokitoci ta kasa, sun tashi tun a yau Talata, 28 ga Afrilu, domin shirye-shiryen tarbar alhazai a Saudiyya.
Hukumar ta kuma shawarci alhazai da su lura cewa jigilar za ta kasance ne rukuni-rukuni, kuma duk kamfanin jirgi zai kammala yankin da aka ba shi kafin ya koma wani. Ta ce duk wanda ya rasa jirginsa a yankinsa dole ne ya ɗauki nauyin jinkiri ko jiran sake haɗa shi zuwa wani rukuni.
