Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A ranar Litinin, Kwamitin Fadar Shugaban ƙasa kan shirin inganta amfani da iskar gas (PCNGi) ya bayyana zuba hannun jarin sama da dala miliyan 450 kan shirin samar da iskar gas samfurin CNG.
Daraktan shirin inganta amfani da iskar gas, Michael Oluwagbemi, ne ya bayyana hakan a yayin wani taro kan makamashi a Nijeriya karo na 9 na rana ta biyu da aka yi a jihar Legas mai taken taron shi ne “Makamashi domin ɗorewar masana’antu”.
Oluwagbemi, wanda Tosin Coker, ya wakilta kuma shugaban sashen kasuwanci na PCNGi, ya ce, shirin ya yi nasarar sauya wa ababen hawa sama da 10,000 injinansu zuwa masu amfani da nau’in samfurin gas na CNG.
“Zuwa shekarar 2027, wannan shiri zai yi nasarar sauya ababen hawa miliyan 1 da suke amfani da man fetur zuwa CNG,” ya faɗa.
Game da fargabar gobarar ababen hawa da ke amfani da iskar gas ɗin CNG, shugaban ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa sun yi ƙoƙari wajen kulawa da dukkan matakai tare da haɗin guiwar wasu hukumomin gwamnati domin kiyaye faruwar hakan.
Ko’odinetan shirin tallafa wa ayyukan raya muhalli wanda ke ƙarƙashin kulawar majalisar ɗinkin duniya, Ibironke Olubamise, ta ce zuba jari kan ayyukan matasa na bunƙasa tattalin arziƙi da inganta muhalli.
Shi ma darakta-janar na hukumar NADDC, Joseph Osanipin, ya ce hukumarsu ta horas da mutane sama da 4,000 kan kan yadda za su sauya abin hawa da ga mai amfani da fetur zuwa mai amfani da iskar CNG.
Ya ce sun fara wani gangamin wayar da kan Nijeriya domin nuna musu alfanun samfurin gas ɗin CNG, inda ya ce, “CNG zai tabbatar da zabtataccen muhalli, ga sauƙi da kowa zai iya amfani da shi.”
Shugaba kuma manajin-darakta na kamfanin, Nord Automobile Ltd., Oluwatobi Ajayi, ya ce kamfanin an kafa shi ne domin kawo ƙarshen ƙaruwar masu son ababen hawa a Afirka da rage dogaro da shigo da kaya.
Ya ce saboda shirin gwamnati da faɗaɗa amfani da iskar gas ta CNG, kamfanin ya shigar da wannan ƙuduri cikin tsarinsa na ƙera ababen hawa ta yadda zai dace da shirin gwamnati.
Hakazalika, manajin-darakta na hukumar kula da kadarori gwamnati a ƙarƙashin ma’aikatar kuɗi (MOFI), Armstrong Tankan, ya ce an kafa kamfanin ne a shekarar 1959 domin kula da kadarorin gwamnatin tarayya.
“A yanzu muna kai ga gano kadarorin gwamnatin tarayya kuma muna ƙoƙarin gwanin mun sahunsu.”
“Muna da kadarori ba iya a nan gida ba, har ma da faɗin duniya bakiɗaya. Kuma yana da muhimmanci mu sanya ido a kansu kayan da suke mallakin gwamnatin tarayya ne kafin mu fara maganar kula da su.”
A cewar Mista Adekunle Makinde, an taron karo na 9 ya samu maƙalu sama da 140 da aka turo daga ƙasashe daban-daban a faɗin Afirka inda kaso 99% na maƙalun da aka turo su ne karonsu na farko kenan.
Sannan an bai wa mutane uku daga suka lashe gasar ƙere-ƙere ta matasa kuma an ba su kyautar kuɗi domin tallafa musu.
“An miƙa kyautar Naira miliyan 2 ga wanda ya ƙera nau’urar sola ta busar da kayan amfanin gona.”
Na biyu kuma an ba shi Naira miliyan 1.5 kan wani abin aikin noman rani inda na ƙarshen aka ba shi Naira miliyan 1 saboda ƙera wata na’urar noman raji da rumbu na zamani a cewar minista.
