Nani ya rataye takalmansa daga wasa ƙwallon ƙafa

Spread the love

Nani ya sanar da yin ritaya daga taka leda a matakin ƙwararren ɗan wasa mai shekara 38.

Tsohon ɗan wasan Manchester United ya rataye takalmansa a Club Estrela Amadora da ke garinsu.

Dan ƙasar Portugal ya buga tamaula a babbar gasar ƙwallon ƙafa ta Turkiya da Sifaniya da Italiya da Australia da kuma Amurka.

Sir Aleɗ Ferguson ne ya ɗauko Nani a 2007 daga Sporting ta Portugal, an kuma sanar da magoya bayan United sayen ɗan ƙwallon tare da Anderson a ranar.

Nani ya bayar da gudunmuwar da United ta lashe Premier League huɗu, ya taka rawar gani da ƙungiyar ta ɗauki Champions League a 2008.

Ya kuma lashe Community Shield a wasan da United ta doke Manchester City a 2011, shi ne ya ci ƙwallon.

Haka kuma ya taka rawar da ta kai United ta ɗauki League Cup biyu da kuma FIFA Club World a 2008.

Nani ya bar Old Trafford zuwa Fernarbahce a 2015 – ya buga wa ƙungiya 10 tamaula a kaka 19 da ya yi a matakin ƙwararren ɗan wasan ƙwallon kafa.

A kakar 2024/25, Nani ya saka hannu kan yarjejeniya a Estrela Amadora.

By ukarofi