Masu ƙananan sana’o’i za su amfana da sabbin dokokin haraji – Shugaban NOA

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babban daraktan hukumar wayar da kan jama’a ta ƙasa, NOA, Lanre Issa-Onilu, a ranar Talata ya bayyana cewa, ƙudirin gyaran dokar harajin da ake shirin yi zai kawar da yawan haraji kuma tagomashi ne ga masu ƙananan sana’o’i a ƙasar.

Mista Issa-Onilu ya bayyana haka ne a yayin wani tattaki na wayar da kan al’umma kan kaucewa son yin arziki da gaggawa da kuma sake fasalin haraji.

Tattakin, wanda ya faro daga harabar Obasanjo ta Sabon-Gari, ya kare ne a ofishin NOA da ke Ladi-Kwali IBB Way a Minna, jihar Neja.

Issa-Onilu, wanda ya samu wakilcin mataimakiyar daraktar kuɗi na hukumar, Mrs Onuoha Uchenna, ya ce ƙudirin na da nufin rage nauyin biyan haraji kan masu ƙananan sana’o’i.

Ta ƙara da cewa sabuwar dokar na nufin masu sana’o’i ba za su riƙe biyan harajai ba, sai dai ka biya haraji daidai iya kuɗin shigar mai sana’a.

By ukarofi