Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An jaddada kira ga ‘ya’yan Jam’iyyar PDP musamman jagorori da masu faɗa a ji su yi haƙuri su taho a haɗa hannu da ƙarfe a gina cigaban jam’iyyar a jihar Kano.
Shugaban Kwamitin Dattawan jam’iyyar na jihar Kano, Alhaji Yahaya Umar Bagobiri ne ya jaddada hakan, ya ce Kano wuri ne da yake da muhimmanci sosai a siyasa, jiha ce da take da faɗi da tasiri da bai kamata ace ana samun rarraba a jam’iyyar da ake ganin ita ce mafita ga al’umma daga halin ƙunci da jam’iyya mai mulki ta jefa su a ciki ba.
Ya ce a matsayinsa na Shugaban Dattawan jam’iyyar ba zai fasa irin wannan kiraye -kiraye ba har sai sun ga ɓaraku da suke da su na cikin gida an ɗinke su, sannan su fito waje su kaɗa bazar su su yi rawa.
Alhaji Yahaya Bagobiri ya ce suna so a ɗauki darasi daga halin da jam’iyyar ta faɗa a baya idan ba a ɗauka ba, sai aga abinda ake so a cimma na gina jihar Kano da tarayyar Nijeriya, matsalolin da ake fama da su na yau da kullum, ace an samu an ɗinke yan ɓarakun, domin su doshi jam’iyyu na adawa, idan hakan bata samu ba kullum su da suke jagorori a jam’iyyar zai zama mabiya su ake wahalar wa da al’umma.
Ya ce amma idan suka haɗa kan su juya kowace irin gwamnati ba wahala ba ne da yardar Allah musamman a wannan yanayi na rashin gamsuwa da mulkin da ake musu a ƙasar nan da ya jefa al’umma a mawuyacin halin rayuwa.
Shugaban Kwamitin na Dattawan na jam’iyyar PDP na jihar Kano, Alhaji Yahaya Bagobiri ya ce ya yi ƙoƙari ya haɗa kan jagorori guda biyu har ya yi magana da su ma, sun zauna sun tattauna kafin a yi zaɓen jam’iyyar na mazaɓu sun yi maganganu da su cewa su yi wa Allah su yi haƙuri a taho a haɗu a haɗa kai a kafa shugabancin mazaɓu 484 da ƙananan hukumomi 44 da jaha kuma har an kai ga za a cimma nasara sai shaiɗanu suka shiga tsakani ba a sami nasara ba.
A daidai wannan lokacin kuma lokaci ya yi da jam’yiyar ta sa jadawalin ta na gudanar da zaɓe kuma ba zata ɗaga ba, shine aka ci gaba da yin zaɓuka kowa ya sai fama fomai,an shiga zaɓe jami’an zaɓe da aka turo aka tabbatar da nasara ga wanda ya ci zaɓe da shaidar jami’an zaɓe daga uwar jam’iyya.
Ya ce tunda ‘yan jam’iyyar PDP ne dukkansu da wanda ya ci zaɓe da wanda bai ci ba, su taho a haɗu a ajiye bambanci koma wanene ya ci zaɓen a matakin mazaɓu da ƙananan hukumomi a zo a haɗu a cigaba da harkokin jam’iiyya shine abinda yakamata domin azo a fitar da al’ummar Kano daga matsaloli da suke ciki.
Ya ce akwai wasu da aka ce sun tafi kotu akan yadda aka gudanar da zaɓe bai musu daɗi ba, domin sun kashe kuɗaɗe sun sai fama fomai suna ganin za su lashe zaɓuka hakan bai samu ba, amma yana ganin duk da shi ba mai shari’a ba ne, idan ka tafi kotu ka kai waɗanda suka shirya zaɓe kara ka ce zaɓe bai yiwu ba, ko ba ayi akan ƙa’ida ba a rushe a sake.
Ya ce “kotu dai ba za ta ɗauki zaɓe ta bai wa mai wara ba, dole jam’iyya zata miƙawa tace a sake gudanar da zaɓe, kila abinda zai faru sai kaga ya faru sama da yanda aka gudanar dai a baya ma , domin dai jam’,iyyar ce dai zata gudanar da zaɓen ba wani sakamako da zaka iya samu, abinda ya faru shi zai sake faruwa, maimakon wannan mai zai hana mu zauna mu haɗa kawunanmu,” cewar Bagobiri.
Alhaji Yahaya Bagobiri ya ce yana fata shugabanni za su ci gaba da tuntubaɓar ‘yan jam’iyya duk wanda yake gani an ɓata masa a bashi haƙuri, wanda yake gani an masa ba daidai ba a bashi haƙuri a jawo sauran al’umma a cigaba da tafiya domin akai ga nasara da yardar Allah.
