Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu ya gargaɗi ‘yan hamayya da sauran ‘yan jihar da su guji sanya siyasa a cikin matsalar tsaro, inda ya nanata cewa hakan na ƙara ta’azzara matsalar a jihar.
Gwamnan ya yi wannan bayanin ne a ƙaramar hukumar Silame a ci gaba zagayen ziyarce-ziyarcen jaje a wuraren da ‘yanbindiga suka kai hare-haren a ‘yan tsakankanin nan.
“Matsalar tsaro al’amari ne mai matuƙar muhimmanci, don haka ya kamata a riƙa bi a hankali a duk lokacin da ake magana game da tsaro,” in ji shi kamar yadda mai magana da yawun gwamnan, Abubakar Bawa ya bayyana.
Ya ce gwamnati ba za ta lamunci yadda wasu suke fakewa da sunan siyasa ko tattauna al’amuran yau da kullum ba suna kawo tsaiko a ƙoƙarin da gwamnati ke yi na tabbatar da tsaro a jihar ta Sakkwato.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa na aiki tuƙuru tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro ba dare ba rana domin samar da tsaro, inda ya ce an fara ganin sakamakon ƙoƙarinsu.
Gwamnan ya nuna takaicinsa kan yadda wasu suke taimako ‘yan bindiga ta hanyar ba su bayanai, inda ya ce akwai buƙatar al’umma su taimaka wa gwamnati ta hanyar ba jami’an tsaro bayanai masu muhimmanci kan harkokin ‘yanbindiga.
A ziyarar, gwamna Aliyu ya ba iyalan duk wanda aka kashe naira miliyan biyu da buhun shinkafa biyar, inda jimilla ya raba naira miliyan 66 da buhun shinkafa 165 a yankin.
