Gwamnatin Shugaba Tinubu ta ware naira biliyan 21 domin bai wa ƴan Najeriya mitocin lantarki kyauta

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamnatin Tarayya ta sanar da ware kimanin naira biliyan ashirin da ɗaya ga kamfanonin wutar lantarki guda 11, domin bai wa ƴan Najeriya masu amfani da lantarki mitoci a kyauta.

Hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasa (NERC), ta faɗi hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar 21 ga watan Yuni, 2024.

Sanarwar ta ce, za’a raba mitocin ne ga waɗanda basu da shi a gidajensu ko wuraren sana’o’insu a ƴan watanni kaɗan masu zuwa.

Hukumar ta ƙara da cewa, wannan huɓɓasa da gwamnatin ta yi, zai taimaka wajen haɓaka asusun kamfanonin ta yadda mitoci za su yawaita a cikin al’umma, sannan zai rage adadin kuɗaɗen bashi da suke kai wa gidajen da makamantansu.

Sannan, hukumar ta ce kamfanonin za su samar wa mutane mitocin ne tare da sanya musu a gidajen su da sauran wuraren da suka cancanta a kyauta.

By Babaji