Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaddamar da shirin horas da ’yan ƙasa miliyan 10 kyauta kan ilimin hada-hadar kuɗi da shigar kuɗi cikin tsari, inda ta ce matasa da mata ne ginshiƙin cin gajiyar yawan al’ummar ƙasar.
Mataimakin Shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana hakan a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, yayin da yake wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce ba za a iya gina tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya ba tare da kwararrun ma’aikata, nagartattun ƙa’idoji da ingantaccen tsarin sana’o’i ba.
A yayin taron, Ofishin Mataimakin Shugaban ƙasa ta hannun Kwamitin Shugaban ƙasa kan Hada-hadar Kuɗi da Tattalin Arziki (PreCEFI) ya rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimta (MoU) da manyan ƙungiyoyin kwararru shida da suka haɗa da ICAN, CIBN, CIS, NICA, CRMI da NIIE.
Yarjejeniyar na da nufin tsara horo, bada takardar shaidar kwarewa, amfani da fasahar zamani da tsarin tallafi domin ƙarfafa gwiwar ’yan kasuwa, musamman mata da matasa. Shettima ya ce hada-hadar kuɗi ba ta tsaya ga samun dama kaɗai ba, sai an samu ilimi, kwarewa da amana.
Shugaban ICAN, Mallam Haruna Nma Yahaya, ya yaba wa gwamnatin Tinubu bisa gyare-gyaren tattalin arziki da suka haifar da ƙaddamar da shirin. Ya tabbatar da cikakken goyon bayan ƙungiyoyin kwararru wajen ganin an cimma nasarar shirin.
Haka nan, Shugaban WAWU Africa, Emmanuel Lennoɗ, ya ce sun shirya samar da dandamalin zamani da kayan aiki da za su tabbatar da ingancin horon. An bayyana cewa shirin na da muhimmanci domin rage ficewar jama’a daga tsarin hada-hadar kuɗi sakamakon karancin ilimi da ƙwarewa.
