Gwamnatin Tarayya ta ba Kanawa 320 aikin duba shiri tare da na’urori

Daga AISHA ASAS

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta ƙaddamar da shirin raba takardun kama aiki tare da na’urorin duba aiki ga waɗanda aka horas domin sanya ido kan ayyukan ma’aikatar a jihar.

An gabatar da taron a ɗakin taro na ‘Coronation’ da ke cikin gidan gwamnati Hall a Kano a ranar 15 ga Yuni, 2021.

Ministar, wadda Babban Sakatare a ma’aikatar, Bashir Nura Alƙali ya wakilta a taron, ta bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙirƙiro Shirin Inganta Rayuwar Jama’a, wato ‘National Social Investment Programme’ (NSIP) ne a cikin 2016 domin a fidda mutane daga ƙangin bauta ta hanyoyi daban-daban da su ka haɗa da tsare-tsare kamar su shirin N-Power da shirin ciyar da ‘yan makaranta da shirin tura agajin kuɗi (CCT) da shirin haɓaka sana’o’i (GEEP).

Ana aiwatar da shirin a jihohi 36 da kuma Yankin Babban Birnin Tarayya.

Ta ci gaba da cewa ma’aikatan sa ido masu zaman kan su guda 320 da aka ɗauka a Kano su na daga cikin mutum 5,000 da aka horas a tsakanin Fabrairu zuwa Afrilu 2021 lokacin da aka yi hidimar horaswar a duk faɗin ƙasar nan.

Ta ce, “Na’urorin da za a yi aiki da su wajen sa ido kan shirin duk a nan Nijeriya aka ƙera su tare da ƙarin wata manhaja mai suna ‘Social Investment Management Information System’ (SIMIS) da wani kamfani na ƙasar nan ya ƙirƙira. “Ta hanyar amfani da wannan manhaja, ma’aikatar ta na kallo da idon ta dukkan ayyukan da ‘yan sa idon ke yi a wajen aiki, ta ga rahotannin da su ka bayar, sannan nasarar da shirin na NSIP ke samu a kowace jiha.

“Hakan zai taimaka wa ma’aikatar ta gane inda ake da matsaloli kuma zai taimaki ma’aikatar wajen cimma burin ta na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara,” inji ta.

Su ma’aikatan sa idon, waɗanda ake kira ‘Independent Monitors’, ana sa ran za su duba aikin wani adadi na masu cin moriyar shirin na NSIP da aka ɗebar masu, waɗanda za a riƙa ba N30,000 kowannen su a duk wata. Sai dai sai an tabbatar da cewa sun yi kashi 80 cikin ɗari na aikin su kafin a biya su alawus ɗin su.

A cikin wasiƙun kama aikin nasu an zayyano duk yadda aikin zai kasance, wanda ya haɗa da: ci gaba da duba shirin na NSIP a yankin ƙaramar hukumar da aka ba su tare da bada rahotanni ƙunshe da shaida kan abin da su ka gano, da sauran su.

Ministar ta gargaɗi ma’aikatan sanya idon da kada su kuskura su bai wa wani daban aikin da aka damƙa masu, domin kuwa kowane ma’aikacin sa ido shi ma’aikatar za ta kama da laifi idan aka aikata ba daidai ba.

Ta taya su murna tare da kira a gare su da su ɗauki wannan aiki da kishin ƙasa, ƙwazo da tsare gaskiya.

Gwamnan Kano, wanda Sakataren Gwamnatin jiha, Usman Alhaji Waziri Gaya ya wakilta, ya yaba wa ma’aikatar saboda yadda ta ke bada goyon baya wajen fitar da ‘yan Nijeriya daga fatara tare da inganta rayuwar su.

Ya faɗa wa ma’aikatan sanya idon cewa su yi amfani da damar da aka ba su wajen kaiwa ga babbar nasara.

Tun da farko sai da jami’i mai kula da shirin na NSIP a Kano, Baba Aminu Zubair, ya ce a gaskiya shirin ya na aiwatar da buƙatar Shugaba Muhammadu Buhari na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara, ya ƙara da cewa Kano ta fi kowace jiha yawan masu cin moriyar shirin na N-Power a duk ƙasar nan.

Aminu ya ce gidaje 119,000 aka yi wa rajista a ƙarƙashin shirin bada tallafin kuɗi na ‘Conditional Cash Transfer’ (CCT) a Jihar Kano masu karɓar N5,000 a kowane wata.

Ya miƙa godiya ga Gwamnatin Tarayya ta hanyar Ma’aikatar Harkokin Agaji da Daɗin Jama’a saboda karamcin da yi.

Sauran waɗanda su ka halarci taron su ne: manyan jami’an gwamnatin jiha, da kodinetocin shirin NSIP daga ƙananan hukumomi da kuma manyan baƙi.