APC ta dakatar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Birnin Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Jam’iyyar APC ta jihar Kano ta ce ta dakatar da ɗan Majalisar Wakilai, Hon. Sha’aban Ibrahim Sharaɗa daga jam’iyya na tsawon shekara guda.

Jam’iyyar ta ce daga wannan lokaci, ta haramta wa ɗan Majalisar shiga harkokinta a dukkanin matakai na tsawon lokacin dakatarwar.

Cikin sanarwar da ta sami sa hannun Shugaban APC na gundumar Sharaɗa, Aljahi Abdullahi Umar da sakatarensa Auwalu Saidu Muhammad, mai ɗauke da kwanan wata 16/06/2021, APC ta ce ta ɗauki matakin dakatar da Hon Sha’aban ne bayan da aka same shi da aikata laifin cin mutuncin Mai Girma Gwamnan Kano da shugabannin jam’iyya daga matakin unguwa har zuwa matakin ƙasa baki ɗaya.

Wanan kuwa ya biyo bayan ƙorafin da magoya bayan APC na gundumar Sharaɗa suka shigar ne a kan ɗan majalisar wanda daga bisani aka kafa kwamitin ladabtarwa na mutum bakwai tare ba shi mako guda don ya binciki lamarin sannan ya miƙa rahotonsa kafin ɗaukar matakin da ya dace.

APC ta ce rahoton binciken kwamitin ya nuna lallai ɗan majalisar ya aikata laifin da aka tuhume shi da aikatawa. Don haka ta ce ta dakatar da shi daga jam’iyya na tsawon watanni 12. Kuma ba ta yarda ya shiga harkokin jam’iyya ba a dukkanin matakai na tsawon lokacin da aka dakatar da shi.

APC ta ce laifin da Hon Sha’aban ya aikata ka iya haifar da rashin jituwa a jihar wanda haka ka iya zama barazana ga kywawan manufofin gwamnan, taɓa mutuncin shugabannin jam’iyya da kuma zama sila na rasa ɗimbin magoya bayan jam’iyya a jihar.