Gwamnatin Tarayya ta fitar da sunayen mutum 50,000 da suka yi nasara a ɗaukar aikin ɗan sanda

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda ta ƙasa (PSC) ta fitar da sunayen waɗanda suka yi nasara a aikin ɗaukar sabbin jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya a matsayin Constables.

Hukumar ta bayyana cewa an kammala aikin ɗaukar ma’aikatan ne cikin tsari mai cike da adalci, gaskiya da kuma bai wa kowa dama ba tare da nuna wariya ba.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Torty Njoku, ya fitar, ya ce an gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Hukumar Federal Character Commission, Ma’aikatar Harkokin ‘Yan Sanda, sassan kula da sana’o’i da shawarwari na jihohi da kuma Kwamitin Hulɗa tsakanin ‘Yan Sanda da Al’umma (PCRC).

Hukumar ta buƙaci duk waɗanda suka rubuta jarabawar aikin ɗaukar ma’aikatan da aka gudanar kwanan nan da su shiga shafin yanar gizon ɗaukar aikin na hukuma mai adireshi: npfapplication.psc.gov.ng domin duba matsayin neman aikinsu.

Sanarwar ta ce za a buɗe shafin ga masu neman aikin daga ƙarfe 12:00 na dare na ranar Alhamis, 16 ga Yulin 2026.

Hukumar ta kuma bayyana cewa waɗanda suka yi nasara za su samu saƙonnin imel da kuma SMS ta hanyar adireshin imel da lambobin wayar da suka bayar lokacin cike fom ɗin neman aikin.

PSC ta ƙara da cewa za a sanar da waɗanda suka yi nasara ranar da lokacin da za su kai rahoto zuwa cibiyoyin horas da ‘yan sanda da aka ware musu domin gudanar da gwajin lafiya da kuma tantance takardu.

Ta yi gargadin cewa duk wanda bai kai rahoto cikin lokacin da aka tanada ba, za a ɗauke shi a matsayin wanda ya yi watsi da damar aikin.

Hukumar ta kuma bayyana cewa duk wanda bai samu nasarar gwajin lafiyar da tawagar likitocin rundunar ‘yan sanda za ta gudanar ba, za a bayyana shi a matsayin wanda bai cancanci ci gaba da horon ba, kuma za a sallame shi daga shirin horaswar.

An kuma bukaci waɗanda suka yi nasara su zo tare da takardar kiran horo, takardar lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN), takardar BVN, asali da kwafin takardun shaidar karatu da sauran takardu da kayan da aka lissafo a shafin ɗaukar aikin.

Shugaban Hukumar PSC, DIG Hashimu Salihu Argungu (mai ritaya), ya gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da ɗaukar sabbin jami’an ‘yan sanda 50,000 domin ƙarfafa tsarin tsaron Nijeriya.

Argungu ya buƙaci waɗanda suka yi nasara su ɗauki wannan dama a matsayin kira na yi wa ƙasa hidima cikin mutunci, gaskiya da jajircewa domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Nijeriya

By ukarofi

Leave a Reply