
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta fara shirin soke dokar ayyana yunƙurin kisan kai a matsayin babban laifi a Nijeriya bayan amincewar da Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta yi da matsayar Ma’aikatar Lafiya da Walwalar ta Tarayya akan al’amarin.
Ƙaramin Ministan Ma’aikatar Lafiya, Dakta Iziaq Salako ne ya bayyana haka a Abuja a ranar Alhamis, yayin bikin Ranar Bayar da Kariya ga Kisan kai ta Duniya ta 2026, wadda aka yi wa taken “Changing the Narrative on Suicide”. Dakta Salako ya ce yanzu an miƙa batun ga Majalisar Dokokin Ƙasa domin gudanar da aikin doka a kai. Ministan, wanda ya samu wakilcin Babban Sakataren ma’aikatar Daju Kachollom S., ya bayyana cewa, za a gudanar da aiki kan al’amarin ne ba tare wani jinkiri ba.
Ya bayyana soke hukuncin babban laifi ga yunƙurin kisan kan a matsayin abin da ya shafi doka da kuma lafiyar al’umma da kariya ga ‘yancin ɗan-adam, yana mai cewa mutanen da suke fuskantar matsalar rashin lafiyar ƙwaƙwalwa suna buƙatar kulawa, tallafi da shiga tsakani yadda ya dace a madadin a hukunta su.
Salako ya kuma ce, amincewar ta FEC akan al’amarin babbar nasara ce musamman ganin yadda majalisar dokoki kaɗai ba za ta iya bayar da kariya ga kisan kai ba, sannan ya jaddada buƙatar zuba jari a ayyukan kula da lafiyar ƙwaƙwalwa, ganowa da wuri da kuma tallafa wa al’umma akan haka gami da wayar musu da kai.
Ya ƙara da cewa, matakin gwamnatin ya yi daidai da Ajandar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ƙoƙarin gwamnatinsa ta inganta fannin lafiya, ceto rayuka da faɗaɗa hanyoyin samun ingantaccen kiwon lafiya.
Ya bayyana cewa, ma’aikatar lafiyan tana cigaba da ƙarfafa harkokinta na ƙasa kan lafiyar ƙwaƙwalwa da kariya ga kisan kai ta muhimman tsare-tsare da matakan shari’a ciki har da dokoki kamar haka: National Mental Health Act, 2021; National Mental Health Policy, 2023; da kuma National Suicide Prevention Strategic Framework 2023 – 2030.
