Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan ma’aikata albashin wata biyar da suke bi bashi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Tarayya na shirin ƙaddamar da biyan ma’aikata kuɗaɗen bashi da N35,000 ga kowannen su har na tsawon wata biyar.

Daraktan yaɗa labarai na Ofishin akanta-janar na ƙasa OAGF, Bawa Mokwa ya bayyana hakan a wata takarda.

Ya ce, da farko dai Gwmantin Tarayya ta biya ma’aikata albashin ne da kaɗan-kaɗan na wa’adin watanni biyar, inda a yanzu ma za a riƙa biyan su N35,000 a kowane wata don biyan su bashin da suke bin ta.

Ya kuma ce, wanda za a fara biya shi ne na watan Afrilun shekarar 2025.

Haka kuma ya ce, gwamnatin ta na iya ƙoƙarinta wajen ganin ta aiwatar da tsare-tsaren kyautata hanyoyin biyan ma’aikata don walwalarsu da kuma ƙara masu ƙwarin-gwiwa wajen sauke nauye-nauyen da aka ɗora masu.

By Babaji