
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya faɗi abinda ya sa shi da Gwamnan jihar na yanzu Sheriff Oborevwori suke koma Jam’iyyar APC daga PDP.
A lokacin da ya ke magana a wani taro da aka yi a Asaba, Babban Birnin jihar, ranar Litinin, Okowa ya ce sun yi hakan ne la’akari da maslahar jihar da al’ummarta.
Ya ce, lallai akwai buƙatar sauya shaƙar da suka yi ganin cewa kowacce al’umma a kan samu wani lokacin da ta ke neman sauyi a ƙoƙarin inganta al’amuranta.
Okowa ya bayyana cewa, matakin zai taimaka wajen ƙara kusanci tsakanin jihar da Gwamnatin Tarayya wajen amfana daga romon demokraɗiyya da ke babban birnin tarayya, Abuja.
Ya kuma ce, a matsayinsa na wanda ya yi gwamna na shekara takwas ya san cewa Gwamna Oborevwori ya na ƙoƙari, don haka ya ke ganin dacewar ya tallafa masa wajen cimma kyawawan manufofinsa ga jihar da al’ummarta.
Ya ƙara da kira ga mambobin jam’iyyar da su haɗa kawunansu wajen ganin sun ciyar da jam’iyyar gaba, ya na mai bayyana kishinsa a matsayin abinda ya sa suka yi hukuncin sauya sheƙar.
