Hukumar ma’aikatan kotu ta Kano ta gargaɗi alƙalai biyu tare da dakatar da magatakarda biyu

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hukumar kula da ma’aikatan kotu ta Jihar Kano ta ɗauki matakin ladabtarwa a kan wasu jami’an kotuna huɗu, inda ta dakatar da wasu magatakarda biyu tare da yin gargaɗi ga alƙalan kotun shari’a biyu bisa nuna rashin ƙwarewa da cin zarafin aikinsu.

Mai magana da yawun hukumar, Baba Jibo Ibrahim ne ya fitar da sanarwar ɗaukar hukuncin ladabtarwar.

Kazalika ya ce, an cimma matsayar ne a yayin taron hukumar karo na 80 da aka gudanar a ranar 22 ga Afrilu, 2025, bisa ga shawarwarin kwamitin korafe-korafen jama’a na ɓangaren shari’a.

Daga cikin waɗanda aka dakatar har da Ibrahim Adamu, babban magatakarda na biyu a babbar kotun shari’a, wanda aka dakatar da shi ba tare da biyansa albashi ba na tsawon watanni shida.

Har ila yau, an ɗage ƙara masa girma bayan da aka same shi da laifin zagi da kuma yunƙurin kai wa na gaba da shi hari wanda ya saɓawa dokokin ma’aikatan Jihar Kano (2004) da kuma dokokin hukumar kula da harkokin shari’a.

A wata shari’ar kuma, Maigida Lawan, babban magatakarda na kotun ɗaukaka ƙara ta shari’a, an hukunta shi ne bisa laifin nema tare da kuma yunƙurin biyan buƙatun kansa ta hanyar da bata dace ba.

Sannan hukumar ta rage masa girma daga mataki na 13 zuwa mataki na 12 sannan ta dakatar da shi ba tare da biyansa albashi ba na tsawon watanni shida, nan take.

Kazalika, alƙalin Kotun shari’ar Musulunci, alƙali Mansur Ibrahim, ya samu gargaɗi a hukumance bayan da aka tabbatar da cewa ya yi kalaman ɓatanci ga mai ƙara.

An kuma gargaɗi abokin aikin sa Alkali Nasiru Ahmad, biyo bayan nuna ɓangaranci a shari’ar da ya yi.

Hukumar ta sake jaddada matsayar ta na yaƙi da cin hanci da rashawa da rashin ɗa’a, inda ta yi gargaɗin cewa, duk wani jami’in kotu da aka samu da aikata rashin ɗa’a zai fuskanci hukuncin ritayar dole.

By ukarofi