Bayan mutuwar aurena na fara sana’ar awara domin ɗaukar nauyin ‘ya’yana – Fatima Isma’il 

Spread the love

“Rashin kulawar mijina ga ‘ya’yana bai sare min gwiwa wurin ba su ilimi ba”

Daga UMAR AKILU MAJERI 

Hajiya Fatima Isma’il Abbas wata mata ce da ta yi fice akan sana’ar yin kosai, awara da kwai da kuma kunun tsamiya da koko wadda ta fara yin wannan sana’ar ta awara tun kimanin shekaru goma sha biyar da suka gabata. 

Hajiya Fatima wadda aka fi sani da Hajiya Magajiya ýar asalin garin Gumel da take zaune a unguwar Zai, kuma take yin sana’arta a kusa da ofishin NEPA a Dutse. A tattaunawar ta da Manhaja, ta shawarci mata su zama masu biyayya, riƙon amana da gaskiya a tsakaninsu da mazajan aurensu. Ta kuma ce koda aurensu ya samu matsala, ba za su yi nadama ba, domin Allah zai ba su mafita ta gari a gaba.

Wakilin Blueprint Manhaja Jihar Jigawa Malam Umar Akilu Majeri, ya samu tattaunawa da Fatima a lokacin da take bakin sana’arta. Don haka idan masu karatu ya shirya, ga yadda tattaunawar ta kasance a tsakaninsu.

MANHAJA: Mai sauraro zai so yabsan sunanki.

FATIMA: Sunana Fatima Ismail, amma wasu na yibmin laƙabi da Magajiya, kuma ni ýar asalin garin Gumel ce a masarautar Gumel anan Jihar Jigawa.

Aure ne ya kawo ni Dutse, bayan mun rabu da mijina na fara yin sana’ar awara domin na ɗauki nauyin karatun ‘ya’yana da kula da kaina kuma in taimaki ‘yan uwana.

Yaushe ne kika fara wannan sana’ar?

Na fara wannan sana’a tun zamanin mulkin Sule Lamido, yana gwamna a hawansa na biyu bayan rabuwa ta da mijina kasancewar mijina ya yi watsi da ni, kuma ya bar min yara bai damu da rayuwarsu ba ko karatunsu.

Saboda bana san yarana su zama ƙasƙantattu, wulaƙantattu ya sa ni kuma na rungumi sana’ar koko, kosai da awara da soya kwai. Da ita ne nake ciyar da kaina, nake wa ‘ya’yan ɗinkin sallah, nake biyan kuɗin makarantarsu da kula da lafiyarsu.

Na ɗauki matakin haka ne domin na ga yarana sun zama masu ilimi domin suma suci gajiyar rayuwarsu kamar yadda sauran yara ke samun kulawar iyayensu a kowanne fanni na rayuwa.

Ni na lura ubansu, wato tsohon mijina na fari kenan, da muka rabu ba mai kishin ‘ya’yana ba ne, ba ya kishinsu, ba ya ƙaunarsu, haka ya ƙaramin ƙwarin gwiwa na in tsaya na baibwa ‘ya’yana kulawa da anan gaba zasu zama masu alfahari da ni a rayuwarsu.

Yaranku nawa ?

Yaranmu uku, mace ɗaya, maza biyu. Dukkansu suna matakin firamare aji biyar da aji uku da aji huɗu kuma zan ci gaba da ɗaukar nauyin karatunsu har su gama karatunsu na firamare zuwa matakin sakandire. Idan matan sun samu miji, ayi masu aure, shi kuwa namijin har digiri sai na ga ya yi. Zan tsaya na ga ya yi karatu.

Da nawa kika fara wannan sana’a ta awara ?

Na fara wannan sana’a da jarin Naira dubu biyar a lokacin waken awaran kwano bai wuce Naira ɗari biyu ba, saɓanin yanzu da ake sayar da kwanon Naira dubu biyu da ɗari biyar. Shi kuma mai bai wuce Naira ɗari uku kwalba ba a wancan lokacin, wadda yanzu ake sayar dashi Naira dubu biyu da ɗari huɗu, wato man ƙuli. 

Yakai ace inabda jari mai yawa, amma saboda tsadar rayuwa yanzu ina sayan kayan sana’a kamar na Naira N300,000 a wata, amma duk a matsayin babshi ake yin sana’ar, sai an biya ake ban kaya.

A duk wata ina sayan waken soya da farin waken kosai, gyero da kayan miya da man girki wadda nake yin sana’a, na Naira dubu ɗari uku wadda a ciki ne nake ci nake sha nake yin dukkan abubuwan rayuwata da kuma ‘ya’yana.

Me ya sa kike ɗaukar nauyin karatun ‘ya’yanki bayan ‘ya’yan naki na da hakki a wajan ubansu ko kuwa zuwa yanzu ba shi a raye?

Yana nan a raye, saidai ya yi watsi da yaran ne, ya fita harkata da su, kuma ba ya tunanin mu sake yin aure koda a nan gaba kamar yadda ni ma bana tunanin sake yin aure da shi, saboda ba ya ƙaunar ‘ya’yana, domin na fuskanci ba shi da adalci. Shi mutun ne marar kishin ‘ya’yansa. Ba ya tunanin sauke nauyin da Allah ya ɗora mar na kula da tarbiyyar ‘ya’yansa domin duk matar da ya rabu da ita, ba ya kula da ‘ya’yanta ko wacce ce.

Bayan kun rabu da shi kin yi wani aure ne?

E, na yi wani auren, na auri wani malamin makaranta, mutumin kirki. Yana so na, ina son shi, amma mahaifiyarsa aka zugata sai da ta raba ni da shi. Yana So na ina sanshi kuma wallahi muna san juna ni da shi har gobe.

Bazan manta da shi ba domin ya nuna min ƙauna, ya kuma nuna wa ‘ya’yana. Yana ba su kulawa, ya ɗauki nauyin karatunsu, sam ba ya nuna min bambanci tsakanin ‘ya’yana da nasa.

Saboda biyayya da ladabi da kissa da soyayya da nake nunamar sai aka riƙa gaya wa mahaifiyarsa cewa ni ƙaruwa ce wai kafin ya aure ni awara nake soyawa agefen titi, hakan ya sa mahaifiyarsa ta ɗauki karan tsana ta washe ni har sai da ta sa ya sake ni.

Mun rabu da juna, amma har yanzu muna gaisuwar mutunci domin shi mutun ne mai daraja, da karamci, bazan iya mantawa da shi ba, domin ya nunabmin ƙauna. Saidai Allah ya biyabshi.

Yanzu kina da aure ?

Fatima ba ni da aure, kuma ina da ra’ayin yin aure, matuƙar na samu wanda na yaba da hankalinsa, kuma zai ba ni kulawa ni da ‘ya’yana, ni kuma zan aure shi mu rufa wa juna asiri. Shi arziki na Allah ne.

Me ya sa ba za ki koma gidan urban ‘ya’yanki ba?

Ai bazan sake koma wa gidan Dan sanda ba, saboda ya azaftar da ni. Ko kaɗan ban ji daɗin zama da shi ba. Ni a yanzu burina Allah yaban mai kyan hali wanda zai kula da ni, amma ni bazan sake zaman aure danshi ba.

Wacce shawara za ki bai wa mata akan yadda za su zauna da mazaje agidan aurensu?

Shawarata nata su zama masu haƙuri, biyayya, ladabi da riƙon amana idan suka tsare gaskiya koda kaddama ta sa sun rabu da mazansu ba za su sha wahalar rayuwa ba, a lokacin da suka koma zaman gida kafin su yi aure kuma Allah zai ba su wasu mazan da suka fi na baya.

Kuma kada mata su manta rashin biyayya da labadi da ƙin yin aiki da gaskiya yana taimakawa wajan yawaitar mace-macen aure a duniya.

Menene shawararki ga ‘ya’ya mata?

Shawara ga mata su guji bin bokaye da miyagun malamai, ‘yan tsubbu domin su ne suke jefa mata cikin halaka. Matuƙar mata suka kiyaye, lashakka Allah zai kiyaye su.

Ko kin lura da cewa, sau da yawa mace idan aurenta ya mutu tana da yara, yaran za su iya zama silar matsalar auren da ta ƙara yi?

Gaskiya ne wani lokacin akan samu hakan, amma sai idan yaran ba su da tarbiyya ko aka yi rashin sa’a taje gidan aka riƙa samun saɓani tsakanin ‘ya’yansa da ‘ya’yanta ana yawan samun tashin hankali to wani lokaci aure yakan samu matsala hartakai ga rabuwa.

Da kuka rabu da mijinki na biyu ya kika ji?

Banji daɗi ba domin musamman akan yadda wasu mutane suke ɓata ni suke kallona amatsayin karuwa, mutuniyar banza wai saboda ina yin sana’ar awara abakin titi.

Ni ba karuwa ba ce, ban san yadda ake yin karuwanci ba ni ba na neman maza, ina yin sana’a ne domin kare mutuncin ‘ya’yana kada su yi talla bana san na zubarwa ‘ya’yana mutunci. Ina yin sana’a ne domin na kare masu daraja su yi karatu su samu ilimi kamar yadda ‘ya’yan kowa suke yi.

Wani abin takaici matan aure ne suke jifana da irin waɗancan kalamai marasa kyau, saboda su ba sa iya yiwa mazansu abinda nake yiwa mijina a lokacin zaman aure wajan kyautatawa saboda haka sai su riƙa jifana da kalmar karuwanci domin su lalata zamanmu da mijina.

Ni na sani wallahi duk abinda ake zargina da shi ni ba na yi, amma irin waɗancan matan da suke ɓata ni sau da yawa sun fi kowa aikata ɓarna dacin amanar mazajensu. Ba ni da burin ɓata kowa, na bar wa Allah ya yi min sakayya.

Mun gode. 

Ni ma na gode.

By ukarofi