Majalisa ta umarci Ma’aikatar Sufuri ta dawo da miliyoyin kuɗaɗen da aka kashe kan tafiye-tafiye ba bisa ƙa’ida ba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kwamitin Majalisar Wakilai da ke kula da Asusun Kuɗaɗen Ƙasa, ya umarci Ma’aikatar Sufuri da ta dawo da N33,563,469.10 ga baitul malin ƙasa, bayan ta gano cewa an kashe su ne ta hanyar yin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje ba bisa ƙa’ida ba.

A ranar Litinin ne kwamitin ƙarƙarshin shugabansa, Bamidele Salam a yayin zaman majalisar, ya bada umarnin bisa rahoton Odita-Janar na shekara 2021.

Rahoton ya bayyana cewa, an biya jami’an ma’aikatar uku Dala 3,000 na alawus don yin tafiye-tafiye zuwan ƙasashen Kenya, Afirka ta Kudu, Moroko, Faransa da Girka ba tare da amincewa ko gabatar da takardun da ke nuna yadda aka yi da kuɗaɗen ba.

Wannan ɗaya ne daga cikin batutuwan sauya akalar kuɗaɗe da rahoton ya bayar akan ma’aikatar.

Sauran sun haɗa da tura wasu kuɗaɗe zuwa ga bankin Shigarwa da Fitarwa na Ƙasa (NEXIM) da adadinsu ya kai Naira miliyan 400.1 da miliyan N93.5 da aka ware don shirye-shiryen horarwa da miliyan N68.6 na tafiye-tafiye da kuma miliyan 11.1 na wasu kwangiloli duk da aka yi su ba akan tsari ba.

A lokacin da ya ke magana kan batun, Daraktan kuɗi na ma’aikatar, Charles Metule, wanda ya wakilci Sakataren Ma’aikatar, ya ce sun tabbatar da kuskuren kuma za su yi ƙoƙarin rage wasu kuɗaɗen haraji a hada-hadar kuɗin ma’aikatar na nan gaba domin tura su ga asusun Gwamantin Tarayya.

Daga nan ne kwamitin ya umarci a gaggauta dawo da kimanin Naira miliyan 11.1 zuwa asusun tarayya.

By Babaji