
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Lahadi ne aka samu wasu ɓata-gari da suka harbe dabbobi 37 a ƙauyen Tashek dake Ƙaramar Hukumar Riyom a Jihar Filato.
Shugaban Ƙungiyar Makiyayan Miyetti ta Ƙasa (MACBAN) reshen jihar, Ibrahim Yusuf Babayo ya bayyana hakan ga wakilin Blueprint a ranar Litinin.
Ya ce, an harbe shanun ne a lokacin da suke kiwo da misalin ƙarfe 1 na rana tare da raunata makiyayinsu.
Daga lokacin ne Babayo ya kira Kwamandan atisayen Operation Safe Haven na yankin Riyom don sanar da shi al’amarin, inda ya gaggauta aika wasu jami’ai wajen da abin ya faru don tabbatarwa.
Ya ƙara da cewa, waɗanda suka aikata laifin, sun yi ne da nufin cimma wata ɓoyayyar manufa.
Ya kuma ce, ya sanar da jagororin ɓangarorin tsaro da suka haɗa da sojoji da kwamishinan ƴan sanda da daraktan Hukumar Ƴan sandan Farin kaya (DSS).
Har’ilayau, ya ce sun neme su da kada su ɗauki doka a hannunsu a yayin da daga ɓangaren jami’an tsaro ake ƙoƙarin kama waɗanda ke da hannu a kai.
