Gwamnatin Yobe na ƙoƙarin inganta harkokin tsaro – Hon. Gubana

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Damaturu

Mataimakin gwamnan Jihar Yobe, Hon. Idi Barde Gubana ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta na aiki tuƙuru wajen magance matsalolin tsaro a faɗin jihar.

Mataimakin Gwamnan ya fadi hakan ne a sa’ilin da yake jagorantar taron tattauna al’ammuran tsaron jihar tare da shugabanin tsaro, a daidai lokacin da gwamnatin jihar ke shirye-shiryen gudanar da taron ƙungiyar gwamnonin Arewa maso Gabas, wanda zai gudana ƙarshen wannan wata na Afirilu.

Hon. Gubana, ya ce gwamnatin jihar ta na aiki tuƙuru tare da jami’an tsaron sojoji da na yan-sanda da sauran su, wajen samar da tsaro mai ɗorewa a faɗin jihar.

Ya ƙara da cewa, “mun haɗu tare da shugabanin jami’an tsaro, don tattauna al’ammuran tsaro, a shirye-shiryen gudanar da taron ƙungiyar gwamnonin Arewa masu Gabas, da zai gudana a ƙarshen wannan wata da farkon wata mai kamawa, a nan Damaturu.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai dangane da abubuwan da taron ya cimma matsaya a kai, Kwamishinan yan-sandan Jihar Yobe, Mista Emmanuel Ado ya bayyana cewa, kwamitin tsaron ya yi bitar batutuwa daban-daban.

“Mun yi cikakken nazari kan yanayin tsaro a watan da ya gabata, yayin da muka fahimci cewa ana samun ci gaba ta fuskar zaman lafiya da ingancin tsaro a faɗin Jihar Yobe.” In ji shi.

A nashi ɓangaren, Mai bai wa gwamnan Jihar Yobe shawara kan al’ammuran tsaro, Janar Dahiru Abdusalam (Mai Ritaya) ya ce gwamnatin Jihar Yobe tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron sojoji, ƴan-sanda da yan-sa-kai, sun yi kyakkyawan shirin samar da tsaro a faɗin jihar.

Sa’ilin da yake amsa tambayoyin manema labarai dangane da halin tsaro a jihar, Janar Dahiru ya ce, duk da mu na fuskantar ƙalubalen tsaro a hanyar Damaturu zuwa Gujba, amma a kowace rana jami’an tsaro su na yin sintiri domin samun cikakken tsaro.

Ya ce ko a kwanan baya, mayaƙan Boko Haram sun kai hari a sansanin sojoji dake Goniri da wani Kamfanin Charlie dake Buni-Yadi a makon da ya gabata.

Dangane da batun karɓar harajin da Boko Haram ke yi a wasu yankunan jihar, ya ce, “Ba za mu ƙaryata zancen ba, musamman yankunan da suke kusa da inda Boko Haram suka kafa sansani.

“A ƙoƙarin daƙile wannan al’amarin, abu ne mai matuƙar wahala, saboda ya taɓa faruwa a Mafa, inda bayan kashe masu karɓar harajin (Boko Haram), daga bisani sun zo, inda suka kashe kusan kowa a ƙauyen. Don haka muna taka- tsan-tsan, kuma dole mu yi kaffa-kaffa.”

“Akwai sojoji, yan- sanda, Civilian JTF da yan-sa-kai, su na nan a kowane lungu da saƙon jihar Yobe, don baiwa mahalarta wannan taron da al’ummar jihar Yobe baki ɗaya, cikakken tsaro.

“Sannan kuma ya dace jama’a su sani, ba za mu iya samun sojoji a ko’ina ba, don haka muna ƙoƙarin fitar da sabbin dabaru da salon yaƙi da yan ta’adda, nan kusan cikin makonni masu zuwa.”

By ukarofi