Akwai yiwuwar Mataimakin gwamnan Neja, Yakubu Garba ya yi murabus

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rahotanni sun bayyana cewa akwai yiwuwar Mataimakin gwamnan Jihar Neja, Yakubu Garba ya sauka daga muƙaminsa.

Sun ce, tuni ya fara tattara kayansa daga gidan da gwamantin jihar ta ba shi a ƙarshen makon da ya gabata, kamar yadda makusantansa suka shaida wa manema labarai.

Haka kuma, an ruwaito cewa wasu sarakunan gargajiya a jihar sun ziyarce shi a ranar Lahadi, inda suka yi ƙoƙarin lallashin sa don ya janye shirin nasa.

Saidai, ba a san ko ya sauya shawarar ba ganin cewa bai furta komai akan hakan ba.

Wata majiya daga ɓangaren mataimakin gwamnan ta bayyana cewa, yunƙurin nasa bai rasa nasaba da tsamin da alaƙarsa ta yi da Gwamnan jihar, Umar Bago.

Ta ce, ya na fuskantar matsalolin rashin girmamawa da ƙiyayya daga gwamnan da mataimakansa.

Wani shaida ya ce, an mayar da mataimakin gwamnan saniyar ware saboda ba a shawartar sa a yayin gudanar da al’amuran da suka shafi gwamnati duk da cewa da shi aka zo kan kujerar.

By Babaji