Ƙungiyar ‘yan jarida ta roƙi ɗan majalisar tarayya ya gina gidan rediyon al’umma a Bichi

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Ƙungiyar ƴan jarida ta Bichi, wato Bichi Journalists Forum ƙarkashin jagorancin shugabanta Musa Yahaya Bichi, ta yi kira da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Bichi Hon. Abubakar Kabir Abubakar da ya gina gidan rediyon al’umma wato (Community Radio) domin wayar da kai da cigaban al’ummar ƙaramar hukumar.

Wannan na cikin wata ziyara da ƙungiyar ta kaiwa Hon. Bichi wanda babban mai taimaka masa a majalisa Hon. Sabo Saye ya wakilta a FCE Bichi a yau Litinin.

Sauran shawarwarin da Ƙungiyar ta bayar sun haɗa da gina wurin kashe gobara na zamani, da kuma kafa kwamitin sa ido kan ayyukan more rayuwa da aka gudanar a ƙaramar hukumar.

Taron wanda ya mayar da hankali kan yadda za a ƙara bunƙasa ayyukan ci gaba a ƙaramar hukumar Bichi.

A yayin ziyarar, shugaban ƙungiyar ta yabawa irin kokarin da Hon. Bichi ya ke kawowa na inganta rayuwar al’ummar ƙaramar hukumar Bichi,

Kazalika Musa Bichi, ya jaddada ƙudurin ƙungiyar na ci gaba da baɗa haɗin kai da kuma yayata ayyukan cigaban garin,

“Muna yaba wa Honorable Abubakar Kabir Abubakar Bichi bisa sadaukarwarsa ga ci gaban al’ummarmu.”

Da yake nasa jawabin, Hon. Sabo Saye ya tabbatar da aniyar Hon. Bichi na ci gaban da kawo ayyuka da yake shafar kowa da kowa, yana mai cewa shawarwarin da aka gabatar sun yi daidai da hangen nesa na mai girma ɗan majalisa na sauya garin Bichi zuwa cikakken gari mai bunƙasa.

“Ƙoƙarin da Ƙungiyar ‘yan jarida ta Bichi ke yi yana nuna burin da jama’armu ke da shi,” in ji Saye.

“Waɗannan shirye-shiryen suna da muhimmanci ga taswirar ci gabanmu, kuma muna maraba da irin wannan haɗin kai domin cimma muradunmu na bai ɗaya.”

Ƙungiyar ‘yan jarida ta Bichi ta jaddada rawar da take takawa a matsayin wani ginshiƙi wajen ƙarfafa zaman lafiya, bin ƙa’idojin aikin jarida, da duk wani ci gaban da ke fitowa daga cikin al’umma a ƙaramar hukumar Bichi.

Ƙungiyar ‘ƴan jarida ta Bichi dai haɗakar ƙwararru ƴan jarida ne da ke da niyyar inganta kyakkyawan shugabanci, tare da kawo sahihin rahotanni da ɗorewar ci gaba ta hanyar wayar da kai da haɗa kan al’umma.

Taron dai ya samu halartar mai taimaka masa ta kan yaɗa labarai Hon. Jamil Master Bichi da kuma ƙwararru ƴan jarida, ƴan asalin ƙaramar hukumar Bichi da suka fito daga radiyo, jarida da gidan talabijin na Jihar Kano.

By ukarofi