Gwamnatin Kano za ta haɗa gwiwa da masana’antar Kannywood don ƙarfafa harkar fina-finai

Spread the love

Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada aniyarta na tallafawa ci gaban harkar fim da inganta ƙwarewar ‘yan fim a masana’antar Kannywood. A wani mataki na musamman, gwamnatin ta ɗauki nauyin horar da mata ‘yan fim guda 50 a fannoni daban-daban kamar shirya fim, bada umarni, rubuta labari, da sauran muhimman fannoni na harkar fim.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana haka a daren jiya a wajen liyafar da aka shirya a Tahir Guest Palace domin karrama matan Kannywood da suka halarci taron horo na kwana uku wanda hukumar tace fina-finan Kano ta shirya.

A jawabinsa, sakatare na hukumar tace fina-finai ta Kano, Alhaji Abba El-Mustapha, ya nuna godiya ga kwamishinan yaɗa labarai Kwamared Waiya bisa goyon bayan da ya bayar wajen cimma nasarar shirin. Haka kuma, ya yabawa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa amincewa da shirin da kuma ƙoƙarin ganin an bai wa matan Kannywood horon da zai basu damar yin gogayya a matakin duniya.

Alhaji El-Mustapha ya buƙaci waɗanda suka amfana da su yi amfani da ƙwarewar da suka samu, su zama jakadu na al’ummar Hausawa da kuma masana’antar Kannywood gaba ɗaya. Ya kuma taya su murna da kasancewa na farko a Arewacin Najeriya da suka samu horo na musamman kan shirya fina-finai ta fuskar bada umarni, rubuce-rubuce, da kuma sarrafa fina-finai.

A nata jawabin, shugabar matan kannywood, Hajiya Hauwa A. Bello, ta bayyana godiya ga Gwamnatin Kano da dukkanin hukumomin da suka bada gudummawa wajen gudanar da shirin. A madadin mata 50 da suka halarci horon, Hajiya Hauwa ta miƙa kyaututtukan godiya ga Sakatare na hukumar tace fina-finai, Kwamishinan yaɗa labarai, da kuma Gwamnan Jihar Kano. Ta bayyana wannan shiri a matsayin wani babban tarihi a masana’antar Kannywood.

By ukarofi