Akwai yiwuwar a koma rubuta jarrabawar WAEC da NECO a komfuta nan da 2026, inji Minista

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya jinjina wa Hukumar Haɗaka ta Kula da bada Gurbin karatu (JAMB), bisa nasarar da ta samu a yayin aikin jarrabawar UTME da ke gudana ta hanyar amfani da komfuta, wato CBT.

Ya ce, daga watan Nuwamban 2025 ne za a fara gudanar da jarrabawar WAEC da NECO ta tsarin CBT kamar yadda ake yi a yayin rubuta na JAMB.

A yayin sanya ido kan jarrabawar UTME a Ƙaramar Hukumar Bwari dake Birnin Tarayya Abuja ne Ministan ya ce, rubuta jarrabawar ta CBT zai taimaka wajen yaƙar satar amsa, wanda a saboda haka ne ya kafa kwamiti da zai samar da tsarin rubuta jarrabawa mai inganci ga ɗalibai a Nijeriya.

Dakta Tunji ya yaba da tsarin CBT da ya gani a cibiyoyin hukumar daban-daban a Nijeriya yayin da ɗalibai suke rubuta jarrabawa, lamarin da ya ce ɗaya ne daga cikin ababen da za su taimaka wajen inganta al’umma, kamar yadda ya ke a tsarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Ya ƙara da cewa, jarrabawar WAEC da NECO da za yi a watannin Mayu da Yunin 2026 za a yi su ne baki ɗaya ta komfuta, saɓanin a takarda da ake yi baya.

A cewarsa, hakan zai taimaka wajen samar da nagartattun ɗalibai da za su yi gogayya da sauran ɗalibai a kowane mataki na karatu s duniya.

By Babaji