
Daga BELLO A. BABAJI
Wasu ƴan bindiga sun farmaki wasu motoci biyu tare da yin garkuwa da matafiya a Ƙauyen Eleyin dake Ƙaramar Hukumar Isin a Jihar Kwara.
Lamarin ya auku ne kwanaki kaɗan bayan aukuwar irinsa a kusa da garin Obbo-Aiyegunle na Karamar Hukumar Ekiti a jihar, wanda ya rutsa da matafiya bakwai da suka nufi Offa daga Abuja.
A ranar Juma’a ne wasu mahara suka kai wani farmakin, inda suka tare wasu motoci biyu tare da yin garkuwa da ƴan cikinsu, waɗanda zuwa lokacin kammala haɗa rahoton, ba a samu bayanin hali ko inda suke ba.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Adetoun Ejire Adeyemi, ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda a yammacin ranar Asabar.
Ta ce, an yi nasarar ceto mutum biyu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su a yayin wani atisayen haɗaka na jami’an sojoji da ƴan bijilante.
Ta kuma ce, ana ƙoƙarin ceto sauran da ke hannu tare da kamo masu hannu a laifin.
Haka kuma ta yi kira ga al’umma da su kwantar da hankula tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai wajen ba su bayanan da za su riƙa taimaka wa ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan ta’addanci a jihar.
