
Daga BELLO A. BABAJI
Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, NDLEA, ta yi nasarar gano maɓoyar miyagun ƙwayoyi a wani otal mai ɗakuna 80, inda ta ƙwace na kimanin sama da Naira biliyan 1, a Victoria Island dake Jihar Legas a yayin wani samame.
A tsakanin ranakun 25 da 26 na watan Afrilu ne lamarin ya auku a otal ɗin mai suna The Hook Hotel, wanda kuma ake kira da Caeser Hotel ko Caeser Lounge a lamba ta 16 dake layin Waziri Ibrahim.
A sanarwar da Kakakin hukumar, Femi Babafemi ya fitar, ya ce jami’ansu a yayin samamen, sun ƙwato buhunan tabar wiwi samfurin Canadian loud guda 589 mai nauyin kilogram 417.3 da kuɗinsa ya kai kimanin N1,042,500,000.
Ya kuma ce, an kama wasu da ake zargin su da hannu a laifin mallakar su da suka haɗa da Haziza Zubairu mai shekaru 42 da Samirat Mustapha mai shekaru 43 da kuma Jamila Salifu ƴar shekara 26.
Ya ƙara da cewa, an ƙwato wasu motoci da dama da suke zargin da su ake aikin safarar kwayoyin da su a otal ɗin gami da telebijin guda 74 da firji 13 da dai sauransu.
A ƴan kwanakin nan dai jami’an hukumar sun yi nasarar kama masu safara ko ta’amali da miyagun ƙwayoyi da wasu haramtattun magunguna a sassa daban-daban na faɗin Nijeriya, a ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan sha da fataucin miyagun ƙwayoyi.
