Gwamnatin Tarayya za ta karrama Sarkin Zazzau da lambar yabo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ganin irin yadda Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, ya ke jajircewa kan al’amuran da suka shafi al’ummar Nijeriya, Ma’aikatar Ayyuka na Musamman da Al’amuran Gwamnati, za ta karrama shi da lambar yabo a matsayin Kwamandan Oda na Tarayyar Nijeriya.

Ministan Ayyuka na Musamman da Al’amuran Gwamnati, Sanata Gorge Akume, ne ya fitar da wannan sanarwar kuma ya rabawa manema labarai a Abuja.

Sanarwar ta ce, “ina da farin cikin sanar da ka kai cewa Shugaban ƙasa Muhammadu Buharl, ya amince da ba ka lambar yabo ta ƙasa, a matsayin Kwamandan Oda na Tarayyar Nijeriya.

“An shirya gudanarwa a bikin ne a Cibiyar Conlerehce International (ICC), da ke Abuja ranar Talata, 11 Oktoba, 2022 da ƙarfe 9:00 na safe.

“An kuma tanadar da masaukin baƙi a Fuller Suites, C80 da ke Abuja,” inji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *